Asisat: 'Yar wasan Barcelona ta yi tsokaci kan Ramadana

Asisat Oshoala, 'yar kwallon Najeriya mai wasa a Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yar kwallon Najeriya Asisat Oshoala da ke taka leda a Barcelona
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tauraruwar 'yar kwallon Najeriya kuma ta ƙungiyar mata ta Barcelona, Asisat Oshoala ta bayyana abin da take ji game da kasancewar yau Juma'a a matsayin ranar azumin Ramadana 29.

Kamar yadda kuke gani, Oshoala ta wallafa a Twitter cewa: "Na 29....#Ramadan".

Sai dai BBC ba ta iya fahimtar me 'yar kwallon ke nufi ba; murna ce ko alhinin rabuwa da Ramadana.

Amma muna fatan ku za ku iya fahimta - musamman ma waɗanda korona ta haramta wa ganawa da abar ƙaunarsu ƙwallon ƙafa.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X