Cikin watan Yuni za a saurari daukaka karar Man City kan hukuncin Uefa

An wallafa

Kotun sauraren kakarrakin wasanni ta duniya, Cas ta tsayar da 8 ga watan Yuni don sauraren daukaka karar da Manchester City ta yi kan hanata shiga gasar Zakarun Turai shekara biyu da Uefa ta yi.

A watan Fabrairu Uefa ta hukunta Manchester City, bayan da ta samu kungiyar da karya dokoki da dama ciki har da ta kashe kudi da ya wuce kima.

City ta musanta aikata karya dokokin hukumar kwallon kafar Turan.

An tsara sauraren daukaka karar daga 8 ga watan Yuni, kuma kwana uku za a yi kafin a yanke hukunci, kuma ba tare da 'yan kallo ba.

Tun lokacin da Uefa ta yanke hukuncin dakatar da Manchester City, kungiyar ta Etihad ta ce za ta daukaka kara.

Uefa ta gudanar da bincike ne, bayan da wata jaridar Jamus, Der Spiegel ta wallafa wasu takardu a watan Nuwambar 2018, inda aka zargi City da kara kudin daukar nauyin tallace-tallace don dagula lissafin hukumar kwallon kafa ta Turai.

Rahoton da tuni City ta yi watsi da shi - an zargi kungiyar da yi wa Uefa rifa-rifa da gangan domin fayyace wa tana kashe kudi kamar yadda dokar hukumar ta tanada.