Leroy Sane: Man City ba za ta bar Sane ya koma Bayern a arha ba

Leroy Sane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rabon da Sane ya buga wa City tamula tun raunin da ya ji a cikin watan Agusta
An wallafa

Manchester City za ta amince Leroy Sane ya karkare yarjejeniyarsa a Etihad, maimakon ta sayar da shi arha ga Bayern Munich.

Bayern ta dade tana zawarcin Sane, bayan da wasu rahotanni ke cewar dan kwallon na son zuwa Jamus da taka leda.

Koci Pep Guardiola ya ce Sane, mai shekara 24 yana daga cikin 'yan kwallon da yake ji da su.

City za ta iya sayar da dan wasan idan an taya shi da tsoka, ba kamar yadda Bayern ta ce za ta biya fam miliyan 35 ba.

Saboda haka kungiyar ta Etihad za ta ci gaba da amfani da dan kwallon a kakar badi, idan har ba a cimma matsaya ba.

Rabon da Sane ya buga wa City kwallo tun raunin da ya yi a gasar Community Shield cikin watan Agusta.

Tsohon dan wasan Schalke na shirin murmurewa ne aka tsayar da wasannin tamaula a Ingila a matan Maris don gudun yada cutar korona.