Arsenal za ta bude filin atisaye domin 'yan wasa su fara motsa jiki

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta amince 'yan wasanta su koma yin takaitaccen atisaye daga mako mai zuwa.
'Yan kwallon za su dunga motsa jiki ba tare da yin cudanya da juna ba, kamar yadda gwamnati ta bukata don gudun yada cutar korona.
Kungiyar ta ce za ta bar 'yan wasa su yi amfani da filin atisaye na London Colney, kuma 'yan kwallon za su dunga bayar da tazara a tsakaninsu.
Arsenal ta amince da ci gaba da rufe wurin atisayen, amma dan wasa shi kadai ake bukata ya kai kanshi sannan ya motsa jiki ba tare da ya kusanci abokin wasa ba, idan wani ma ya je atisayen.
Hakan ya biyo bayan da Arsenal ta yi taro da 'yan wasa kan yadda ya kamata su koma motsa jiki, bayan da aka dauki hoton Alexandre Lacazette da David Luiz da Nicolas Pepe da kuma Granit Xhaka sun karya dokar bayar da tazara.
An ga Lacazette da wani mutum da ke cikin mota suna magana ba tare da tazara ba, shi kuwa Luiz da Xhaka suna wasan banza a wurin shakatawa.
Shi kuwa Pepe an dauki hotonsa yana buga tamaula tare da wasu abokansa.
Arsenal ta gargadi 'yan wasan da dukkan wadanda ke mata aiki da su dauki matakan kariya su kuma bi doka kamar yadda aka tsara.
Gwamnatin Burtaniya ta amince dan wasa zai iya atisaye shi kadai ko tare da wadanda suke gida daya ko wuri daya a killace, idan kuma za su fita waje ya kamata ku bayar da tazara a tsakaninsu.











