Coronavirus: Yadda aka mayar da filin wasa asibiti a Nigeria

A fadin duniya, an mayar da filayen wasa asibitocin bayar da kulawar gaggawa yayin da yaduwar annobar coronavirus ta sa asibitoci suka yi kadan kuma ma'aikatan lafiya suka rasa wuraren da za su sa marasa lafiyar da yawansu ke karuwa.
Ganin yadda suke da sarari sosai, ana ganin filayen wasa a matsayin wuraren da suka dace a kafa asibitocin wucin gadi.
Don haka bayan shekara biyu ana aikin gyara shi, filin wasa na Onikan da ke Legas a Najeriya - wanda ya kamata ya zama cibiyar wasanni a kasar - a yanzu, za a bude shi a matsayin wurin killace masu fama da cutar Covid-19.
Legas ce cibiyar annobar a Najeriya - kuma jihar, wadda ta samu kanta a wani yanayi na neman inda za ta kafa cibiyoyin killace masu dauke da cutar, ta mayar da filin wasan mai iya daukar mutum 5,000 zuwa asibiti, a kokarinta na yaki da yaduwar cutar.
Filin wasan na iya daukar gadajen asibiti 110, kuma gwamnatin jihar Legas ce ta gina shi tare da hadin gwiwar wani banki, don rage nauyi ga cibiyar killace masu dauke da cututuka masu yaduwa da ke Yaba.
Tsohon Shugaban harkokin wasanni na jihar, Kweku Tandoh, ya kare matakin amfani da filin wasan bayan sukar da wasu 'yan jarida a bangaren wasanni suka yi wa matakin, wadanda ke ganin rashin dacewarsa.
"Babu wani laifi don an yi amfani da filin wasan saboda wannan lamari na gaggawa," ya ce wa BBC.
"Abu ne da ake yi a fadin duniya. Ana amfani da filayen wasa na Real Madrid da na Maracana duk a matsayin asibitoci na wucin gadi.
A lokaci na annoba, akwai abubuwan da ba za a iya ja ni-in-ja ka ba a kansu saboda sun shafi lafiyar mutane.
"A Amurka, lokacin da aka yi Guguwar Katrina, an yi amfani da filayen wasa a Louisiana wajen ajiye mutanen da guguwar ta raba da muhallansu."

Amma wani dan jarida a bangaren wasanni da ke zaune a Legas, Kelechi Nkoro ya ce yana da tantama kan matakin, inda ya ce da an yi amfani da Dandalin Tafawa Balewa mai girman hekta 14.5 wanda kuma jihar ke amfani da shi wurin shagulgulanta.
"Ina goyon bayan mayar da wuraren gwamnati a matsayin cibiyoyin kula da lafiya a wannan lokaci - babu abin da ya kai rayuwa muhimmanci - amma a Najeriya, muna da filayen da ke da sarari kuma a kusa da filin wasa na Onikan," a cewarsa.
"Ai da su aka fara dubawa. Me ya sa aka fara batun filin wasan?"
Damuwarsa ita ca wannan mataki zai iya lalata filin wasan sosai kuma ba lallai ne a gyara shi ba idan annobar ta gushe.
"Babu shakka ana amfani da wasu filayen wasa a sauran sassan duniya lokacin wannan annoba, amma dama can rashin kula da filin wasa babbar illa ce ga wasanni a Najeriya," a cewarsa.
"Za a gyara illar da aka yi wa filin wasan nan idan muka ga bayan annobar?"

Kungiyar kwallon kafa ta Brazil, Santos, ta sanar da cewa za a kafa wani asibiti na wucin gadi a daya daga cikin dakunan shakatawarta a cikin filin wasa na Vila Belmiro, yayin da kungiyar Real Madrid ta kafa gadajen asibiti 5,000 a dakin taron kungiyar na IFEMA da kuma wani bangare na filin wasan da ake amfani da shi wajen ajiyewa da rarraba kayan kiwon lafiy
A Ingila, kungiyar Tottenham Hotspur ta bayar da damar amfani da wani wurin ajiye motoci da aka gina a karkashin filin wasanta don ajiye abinci, yayin da kungiyar kwallon kafa ta Burnley ta bi sahu ta hanyar bai wa asibitin East Lancs damar amfani da wani bangare na filin wasan Turf Moor.
Cibiyar Billie Jean King ta wasan Tennis, wadda ta yi suna wajen daukar nauyin gasar US Open, ta cimma yarjejeniya da gwamnatin New York don amfani da cibiyar hotronta a matsayin asibiti na wucin gadi.
Tandoh ya ce ba za a yi wa harabar filin wasan na Onikan illa sosai ba saboda ciyawar da ke filin hadi ne na ciyawar gaske da ta roba, ba kamar a ce ciyawar gaske ce zalla ba. a.










