Barca na son dauko Aubameyang, Ronaldo ba zai bi Bechham Inter Miami ba

Barcelona are eyeing Arsenal's Pierre-Emerick Aubameyang

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Barcelona na sanya ido sosai a kan dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, wanda kwantaraginsa zai kare a karshen kakar wasa mai zuwa. (Sunday Express)

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, ya ce yana cike da farin ciki a Juventus kuma ba ya shirin komawa sabon kulob din David Beckham Inter Miami. (Sky Sports)

A shirye Manchester United take ta biya £150,000 a duk mako domin dauko kyaftin din Aston Villa, Jack Grealish, a bazara. (Sun)

Chelsea ta bi sahun Liverpool, Manchester United da Tottenham wurin sanya ido kan dan wasan Canada Jonathan David, wanda farashinsa ya kai £20m. Dan wasan mai shekara 20 ya zura kwallo 23 a wasan da ya buga wa Gent a kakar bana. (Sunday Express)

Liverpool za ta inganta gabanta a bazara inda take son sayo dan wasan Ingila Adam Lallana, mai shekara 31, da dan kasar Switzerland Xherdan Shaqiri, mai shekara 28, wadanda ake sa ran za su bar kungiyoyinsu a karshen kakar wasan bana. (The Athletic via Express)

Ya kamata dan wasan Watford Abdoulaye Doucoure, mai shekara 27 ya zama cikin sawun gaba da Liverpool za ta dauko, a cewar tsohon kocin Ingila Owen Hargreaves (Daily Star)

Sai Manchester City ta biya £40m idan tana son dauko dan wasan Everton mai shekara 23 Mason Holgate. (Football Insider)

Dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland zai kasance zabin farko da Real Madrid za ta yi idan za ta dauko sabon dan wasan gaba a baraza uku a jere. Madrid ta san cewa sai ta biya £65m a kan dan wasan mai shekara 19. . (Marca, in Spanish)

Kazalika, dan wasan RB Leipzig Timo Werner, mai shekara 23, na cikin 'yan wasan da Real Madrid ke son daukowa, abin da ke nufin Liverpool za ta fuskanci hamayya wurin sayo dan kasar ta Jamus wanda farashinsa ya kai £51m. (Daily Mail)