Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Benzema da Bale ba za su yi wa Real Super Cup ba
Real Madrid za ta fafata da Valencia ba tare da Gareth Bale da Karim Benzema a wasan daf da karshe a Super Cup da za su kara a Saudi Arabia.
Bale dan kwallon tawagar Wales na fama da rashin lafiya, yayin da dan wasan tawagar Faransa, Benzema ya ji rauni a kafa.
Wasa daya kacal Benzema bai buga wa Real Madrid ba a bana a fafatawar da ta yi da Osasuna wasan mako na shida a La Liga a Bernabeu.
Madrid ta hutar da dan kwallon ne a ranar, duk da ta fito da shi a kan benci a karawar da Osasuna.
Bale da Benzema ba su bi Real zuwa Saudi Arabia ba ranar Litinin, inda suka zauna yin jinya a Spaniya.
Haka shima Eden Hazard da kuma Marco Asensio na jinya.