Wikki ta ragargaji Lobi Stars da ruwan kwallaye

An wallafa

Wikki Tourists ta caskara Lobi Stars da ci 4-0 a wasan mako na 20 a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya da suka kara a Bauchi ranar Lahadi.

Wikki ta ci kwallon farko ta hannun Manu Garba minti uku da fara wasa, haka kuma ya kara na biyu na wasan.

Haka kuma Idris Guda shima ya ci wa Wikki kwallo biyu a fafatawar da ya bai wa kungiyar hada maki uku masu kyau.

Da wannan nasarar Wikki ta koma ta 12 a teburi da maki 25, bayan da ta buga karawa 20.

Plateau United ta koma ta daya a teburin Firimiyar, bayan da ta ci Dakkata 2-0, karo na biyu kenan da Dakkata ta yi rashin nasara a wasan waje, na farko shi ne a gidan Mountain of Fire.

Kano Pillars kuwa 1-0 ta doke Mountain of Fire, wadda ta zura mata kwallo 3-0 a wasan mako na 19 ta kuma taka mata burkin buga wasa 13 a jere ba tare da an doke ta ba.

Nasarawa United ta dan yi sama zuwa mataki na 19 daga na 20, bayan da ta ci Jigawa Golden Stars 1-0.

Adamawa United ce ta koma ta karshe ta 20, bayan da Heartland ta sharara mata kwallo 5-0.

Sakamakon wasannin mako na 20 da aka buga:

  • Rangers 1-2 Akwa United
  • FC Ifeanyiubah 3-1 Sunshine Stars
  • Heartland 5-0 Adamawa United
  • Kano Pillars 1-0 MFM
  • Kwara Utd 1-1 Rivers United
  • Plateau United 2-0 Dakkada
  • Nasarawa United 1-0 Jigawa Golden Stars

Warri Wolves 2-0 Katsina United