Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
MFM ta taka wa Kano Pillars burki a gasar Firimiya
Mountain of Fire and Miracle ta doke Kano Pillars da ci 3-1 a wasan mako na 19 a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya da suka kara ranar Lahadi.
Pillars ce ta fara cin kwallo ta hannun Auwalu Ali saura minti 11 a je hutu.
MFM ta farke kwallon farko ta hannun Adewole Adeniji a minti na bakwai da komawa zagaye na biyu.
Clement Ogwu ya ci wa MFM kwallo na biyu, sannan shi ne dai ya kara na uku saura minti na tara a tashi daga karawar.
Da wannan sakamakon MFM ta takawa Pillars burki, bayan wasa 13 a jere da ta yi ba tare da an doke ta ba a gasar Firimiyar ta Najeriya.
A mako na 18 Pillars ta ci Adamawa 2-0 a Kano, kuma ita ce karawa ta 13 a jere ba tare da an doke kungiyar ba.
Rabon da a doke Pillars tun ranar 20 ga watan Nuwamba, inda Jigawa Golden Stars ta yi nasara da ci 1-0.
Sai dai kuma Pillars tana da kwantan wasa biyu da za ta yi da Enugu Rangers da kuma Enyimba, wadan da suke buga gasar Zakarun Afirka ta Confederation.
Sauran sakamakon wasannin da aka buga:
- Lobi 2-1 Wikki
- Katsina Utd 2-1 Wolves
- Jigawa GS 1-0 Nasarawa
- Rivers Utd 1-0 Kwara Utd
- Akwa Utd 0-0 Rangers
- Enyimba 2-1 Abia Warriors
- Adamawa Utd 1-0 Heartland
- Sunshine Stars 2-0 FC IfeanyiUbah
Tun a ranar Asabar Dakkada da Plateau United suka tashi wasa 0-0