An kammala zangon farko a gasar Firimiyar Najeriya

An wallafa

A karshen mako ne aka karkare karawar zangon farko a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya, wadda aka yi wasanni 19.

Yadda kungiyoyi ke zuwa waje su ci wasa ya karawa gasar bana armashi, ganin an yi nasara a wasanni 23.

A kakar 2015 aka kafa tarihin cin wasa 31 da kungiyoyi suka je suka ci wasanninsu, amma a zangon farko kuma nasara 19 kungiyoyin waje suka samu.

Kungiyar Dakkada ita ce tilo da ta yi rashin nasara a wasa daya a waje a bana, shi ne wanda ta yi da Mountain of Fire.

Haka kuma a kalla kungiyoyi 15 sun ci wasa daya ko biyu a waje, bayan da aka kammala zangon farko.

Kano Pillars ta yi wasan Firimiya 13 a jere ba tare da an doke ta ba, sai a karawar mako na 19 ta sha kashi a hannun MFM da ci 3-1 a jihar Legas.

Wani bincike ya fayyace cewar kungiyar da take ta daya a zangon farko ita ce ke lashe kofin inda aka ci takwas daga 10 a baya masu jan ragamar teburi.

Lobi Stas ce ta daya kawo yanzu da maki 35, sai Plateau United ta biyu mai maki 33, yayin da Rivers United mai maki 32 ita ce ta uku a teburin.

Wadanda suke kasan teburi su hudu kuwa sun hada da Jigawa Golden Stars ta 17 mai wasa 18 da maki 20.

Rangers ce ta 18 mai kwantan wasa biyar da maki 17, ita ma Adamawa United maki 17 ne da ita a mataki na 19.

Nasarawa United ce ta karshe ta 20 mai kwantan wasa daya da maki 16.

Kwantan wasannin da za a yi ranar Laraba:

  • Rangers da Jigawa kwantan wasan mako na bakwai
  • Enyimba da Wikki kwantan wasan mako na 11
  • Akwa United da Dakkada kwantan wasan mako na 13