Soares ya koma Arsenal a matsayin aro

Asalin hoton, Getty Images
Kulob din Arsenal ya dauki dan wasan bayan Portugal da ke murza leda a Southampton wato Cedric Soares a matsayin aro.
Dan wasan mai shekara 28 ya buga wa tsohuwar tawagar tasa Southampton wasanni 100 tun bayan da ya koma kungiyar a 2015.
Ya kuma wakilci kasarsa sau 33 ciki har da a wasannin da Portugal ta buga a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a 2018, da kuma gasar kasashen nahiyar turai da Portugal ta lashe a 2016.
Hukumomin Arsenal sun bayyana dan wasan a matsayin zakakuri wanda zai kara wa tawagarsu karfi.
Dan wasan ya soma murza leda ne a Sporting Lisbon, kuma ya zama dan wasa na biyu da Arsenal ta saya a kakar musayar 'yan wasan bana, bayan ga dan wasan bayan Plamengo Pablo Mari da shi ma ya koma kungiyar.







