Kociyan Man Utd da Van Persie na cacar-baki

An wallafa

Kociyan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce tsohon dan wasan kungiyar Robin van Persie ba shi da 'yancin sukar tsarin koyarwarsa.

An ruwaito Van Persie yana cewa ba ya jin dadin tsarin aikin Solskjaer, a wata hira da ya yi da BT Sport, bayan wasan da Arsenal ta doke United da ci 2-0, ranar Laraba.

A hirar dan wasan na Holland, ya ce: ''Wannan ba lokaci ba ne da za a yi fara'a.''

A martanin da ya mayar wa Van Persie, ranar Juma'a Solskjaer, ya ce, "Ban san Robin ba kuma Robin bai san ni ba."

"Kusan ba shi da wani 'yanci na sukar tsarin jagorancina, kuma b azan sauya yadda nake ba."

Van Persie ya dauki kofin gasar Premier da Manchester United bayan da ya koma kungiyar daga Arsenal a shekarar 2012.

Ya taka wa kungiyar leda sau 86, inda ya ci mata kwallo 48, kafin ya koma kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya a shekarar 2015.

Shi kuwa Solskjaer ya ci wa kungiyar ta Manchester United bal 91 a wasa 235 da ya yi mata a tsakanin 1996 da 2007.

Solskjaer ya ce, "Eh Robin, ya dauki [jesina] lambata, 20 kuma ina ganin abin da zai dauka daga gare ni ke nan.''

A yanzu Manchester United tana matsayi na biyar a teburin Premier, inda take bin Chelsea, ta hudu da maki hudu a tsakaninsu.

Kuma a bana har yanzu kungiyar ba ta ci wasan Premier uku ba a jere.

Za ta kara da Wolves a wasan mataki na uku na gasar cin kofin Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila a ranar Asabar.