EURO 2020: Ireland ta ce tana da kwarin gwiwar casa Denmark

Mick McCarthy zai yi kokarin samun nasara a kan takwaransa dan kasar Denmark Age Hareide a Dublin

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Mick McCarthy zai yi kokarin samun nasara a kan takwaransa dan kasar Denmark Age Hareide a Dublin
An wallafa

Kocin Ireland Mick McCarthy ya ce yana da kwarin gwiwar tawagarsa za ta samu galaba a kan Denmark a wasan neman gurbin shiga gasar Euro 2020.

Denmark ce ta fitar da Ireland a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya, yayin da take mataki na 14 a duniya a jadawalin kasashen da FIFA ta fitar.

Sai dai McCarthy ya yi amanna cewa za su samu galaba a kan kasar a wasan da za su kara ranar Litinin a birnin Dublin.

"Kodayaushe akwai babban wasan da yake tunkararmu kuma muna da yakinin za mu samu nasara. Idan har ban yarda da hakan ba, da tuni na wuce gida abina," in ji McCarthy.

Karo na shida ke nan zai kasance da kasashen za su fafata a cikin shekaru biyu, kuma babu wasan da Ireland ta samu nasara a kai.

Wasa hudu ta yi canjaras da Denmark din sai guda da ta yi rashin nasara a kai.

Amma McCarthy ya ce yana da tabbacin za su samu galaba a kan kasar.

Ba tare da la'akari da sakamakon na Litinin ba, jamhuriyar Ireland za ta samu damar buga wasan Euro 2020 a watan Maris.