Ronaldo bai tabuka komai ba a shekara 3 - Capello

An wallafa

Cristiano Ronaldo ya nuna bacin rai bayan an sauya shi kuma bai zauna a benci ba, abin da ya jawo tsohon mai horarwa Fabio Capello ya soki dan wasan gaban na Juventus da cewa kokarinsa ya ragu a cikin shekara uku da suka gabata.

Dan kasar Portugal mai shekara 34, Ronaldo ya nuna bacin ransa ne bayan an sauya shi a wasan da Juve ta doke AC Milan 1-0, karo na biyu kenan da ake canjinsa a jere.

"[Cristiano] zakara ne, babu wanda yake da ja kan haka. Sai dai a tsawon shekara uku da suka gabata bai yanke wani dan wasa ba," Capello ya fada a kafar talabijin ta Sky Sport Italia.

"A yanzu ba ya kan ganiyarsa saboda haka ba wani abu ba ne idan aka sauya shi.

"Ba sai Sarri ya yi wata tantama ba kafin ya cire shi. Abin da ya yi bai kamata ba [na kin zama a kan benci bayan an sauya shi] kuma ya yi sa-in-sa da kocinsa Sarri.

"Ya kamata mutum ya zama zakara hatta a lokacin da aka yi canjinsa ba wai sai lokacin da abubuwa suke tafiya yadda ake so ba. Dole ne ya girmama abokan wasansa."

A bangarensa, mai horarwa Sarri ya yi magana kan abin da Ronaldo ya aikata kuma ya nuna kwarin gwiwarsa kan 'yan wasansa.

"Abin da aka saba ne dan wasa ya yi fushi idan an yi canjinsa musamman idan yana kokari sosai," in ji Sarri. "Hakan ma yana dadada wa mai horarwa."