Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ba za ta kori Emery ba, Kante ba zai je Madrid ba
Jaridar The Athletic ta ruwaito cewa shugabannin kungiyar Arsenal suna goyon bayan Unai Emery 100% bisa 100% sannan kuma sun tsara cewa za su jira har zuwa karshen kakar bana kafin su yanke wani hukunci.
Kazalika jaridar The Times ma ta ce Emery ba ya fuskantar wani matsi a Arsenal din.
Har wa yau, tsohon kocin Barcelona Luis Enrique, wanda kuma ake alakantawa da aikin horar da Arsenal din ba zai dawo aikin horararwa ba a nan kusa. (ESPN)
Dan wasan tsakiyar Chelsea N'Golo Kante mai shekara 28 ya nisanta kansa daga rahotannin da ke cewa zai koma Real Madrid har ma ya ce akwai yiwuwar ya yi ritaya a Chelsea din. (Sun)
Manchester United ka iya dawo da tsohon dan wasan gabanta Zlatan Ibrahimovic mai shekara 38 kuma dan kasar Sewden. Saura kadan dai kwantaragin dan wasan ya kare da kungiyarsa ta LA Galaxy ta kasar Amurka. (TuttoMercatoWeb, via Mail)
Tottenham za ta yi yunkurin daukar dan wasan Ajax Hakim Ziyech mai shekara 26 idan har Christian Eriksen, mai shekara 27, ya bar kulob din. (90min)
Mahaifin dan wasan PSG Neymar ya ce ba zai sake tattaunawa da Barcelona ba game da komawar dansa kulob din sannan ya ce dan nasa zai ci gaba da zama a Paris St-Germain. (ESPN Brazil, via Mail)
Tsohon mai horarwa Fabio Capello ya ce salon wasan Cristiano Ronaldo ya yi kasa a cikin shekara uku da suka gabata. (Marca)