Guardiola ya ce babu tabbas ko za su kamo Liverpool a teburi

An wallafa

Pep Guardiola ya ce "ba shi da tabbas" ko kungiyarsa ta Manchester City za ta kamo Liverpool, wadda ke saman teburi da tazarar maki tara tsakaninta da City, wadda ke mataki na hudu.

Man City dai tana yunkurin zama kulob na farko da zai lashe kofin Premier sau uku a jere tun bayan Manchester United a shekarar 2009.

"Ni ba boka ba ne, ban san me zai faru nan gaba ba," in ji Guardiola. "Wasannmu na gaba da Chelsea ne, za mu yi bakin kokarinmu mu doke su."

Matsayin da Man City take a yanzu yana daidai da wanda take kai a bara war haka, lokacin da Liverpool ta ba ta tazarar maki 10 cikin wasa 20 duk da cewa Liverpool din ta fi ta buga wasa a lokacin.

Sai dai, tun daga wannan lokaci City ta shiga cin wasanni ba ji ba gani, inda maki uku kawai ta rasa a ragowar wasa 18 da ta buga, ciki har da wanda ta cinye Liverpool a filin wasa na Etihad.

Sai dai a bana abin bai yi wa City kyau ba yayin da 'yan wasanta suka rika sowar cewa Alexander-Arnold ya taba kwallo da hannu a cikin yadi na 18 dakikoki kadan kafin Fabinho ya ci kwallon farko.

Ran Guardiola ya baci sosai da hukuncin kuma ya nuna cewa duk wani zargi yana kan Mike Riley ne, wanda shi ne shugaban kungiyar alkalan wasa ta Professional Game Match Officials Limited, wadda ita ce ke da alhakin kula da alkalancin wasa a Ingila.

Da aka tambaye shi game da hukuncin sai ya ce: "Tambayi Mike Riley da abokan aikinsa."