Barcelona: An kori Victor Valdes a matsayin kocin matasa

Victor Valdes

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan Yuli Valdes ya karbi aikin
An wallafa

Barcelona ta kori kocin kungiyar ta matasa 'yan kasa da shekara 19, Victor Valdes, bayan wata uku da karbar aikin.

Victor Valdes wanda ya karbi aikin a watan Yuli, kungiyar ta maye gurbinsa da Franc Artiga bayan wata rashin jituwa tsakaninsa da Patrick Kluivert, wanda shi ne sahugaban kungiyar.

An hana Valdes jagorantar kungiyar a karshen mako ne bisa binciken da tsohon tauraron Barcelona Kluivert yake yi a kan kocin.

A wani bayani da kungiyar ta vwallafa a shafinta, ta ce: "Victor Valdes, kocin tawagar Juvenil A, ba zai jagoranci tawagar ba a wasan da za ta yi da Gimnastic de Tarragona a filin wasa na Municipal Camp de la Pobla de Mafumet."

Tsohon mai tsaron ragar, mai shekara 37, ya lashe kofin La Liga shida da kuma Zakarun Turai na Champions League uku yayin zamansa a Barcelona.

Tsohon golan Man United din ya gamu da ikon Kluivert, abin da ya yi sanadiyyar kawo karshen aikinsa.

Valdes da Kluivert sun yi wasa tare a Barcelona a shekarar 2002 kafin Kluivert ya koma Newcastle.