Lionel Messi: Alkadarin Pele ya kusa karyewa

Asalin hoton, Getty Images
Hamshakin tauraron dan wasa Lionel Messi na kan hanyar karya tarihin da aka yi imanin cewa ba zai karyu ba na kwallo 643 da shahararren dan wasan Brazil Pelé ya ci wa kungiyar Santos ta Brazil din a tsawon shekara 18.
Yanzu haka saura kwallo 39 Messi ya kamo waccan lamba da Pele ya gindaya.
Kuna mamaki an ce saura kwallo 39? To saurari wannan:
Kwallon da Messi ya ci a wasansu da Sevilla a daren Lahadi - ta farko kenan a La Ligar bana - ita ce ta 604 a Barcelona.
Ganin cewa ya ci wa Barcelona kwallo sama da 40 a kowacce kakar wasa 10 da ya buga, dan shekara 32 din a shirye yake tsaf ya karya alkadarin Pele a kakar bana.
Kafin zuwan Messi harkar kwallon kafa ba a taba tsammanin akwai wanda zai kamo Pele ba a tarihin da ya kafa a shekarun 1956 zuwa 1974.
Dan wasan Bayern Munich Gerd Müller ne kadai ya kusa kai wa ga gaci, inda ya ci wa Bayern din 565 daga 1964 zuwa 1979.
Tun bayan da ya saka jesin Barcelona a shekarar 2004, Messi ya zura kwallo 420 a La Liga, 112 a Champions League, 51 a Copa del Rey, 13 a Spanish Super Cup, biyar a Club World Cup sai kuma uku a UEFA Super Cup.







