Dogon Mai Takwasara ya sha kisa a hannun Dan Jere
An wallafa
Wasanni da dama aka kara a gidan wasa na Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Najeriya a safiyar Lahadi.
Wasannin da suka yi kisa:
Shagon Na Master Ali ya doke Shagon Saiwa
Autan Mai Takwasara ya buge Garkuwan Shagon KK
Bahagon Damba ya yi nasara a kan Shagon Bahagon Na Dutsen Mari
Taufik Garkuwan Ebola ya kashe Shagon Ali Kanin Bello
Shagon Yalo Dan Suru ya buge Na Sigari
Wasannin da babu kisa kuwa:
Shagon Matawallen Kwarkwada da Shagon Shagon Alhazai
Garkuwan Autan Faya da Shagon Garkuwan Cindo
Shagon Sojan Kyallu da Shagon Bahagon Fijot
Autan Faya da Shagon da Shagon Bahagon Bama
Shagon Garba Dan Malumfashi da Shagon Na Sigari