Diego Maradona: Shararren dan wasan Argentina zai horas da Gimnasia

Diego Maradona at Dorados

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Maradona ya taba horas da kungiyar Dorados ta Mexico
An wallafa

An bayyana shahararren tsohon dan wasan kwallon kafa na Argentina Diego Maradona a matsayin kocin kungiyar Gimnasia.

Maradona mai shekara 58, shi ne jagoran kungiyar kwallon kafa ta Argentina da ta lashe gasar cin kofin duniya a 1986, zai horas da kungiyar ne zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Kungiyar Gimnasia, wadda aka lakaba wa sunan El Lobo tana matakin karshe ne Lig na Primera na Argentina.

Kungiyar na da maki daya ne kacal a wasanni biyar na baya da suka buga.

Maradona ya ajiye aikin horas da kungiyar Dorados ta Mexixo a watan Yuni saboda dalilan rashin lafiya.

Maradona ya wallafa a shafinsa na Twitter: "A karshe dai komai ya tabbata, Ina matukar farin cikin kasancewa sabon kocin Gimnasia."

Wannan ne aikin horar da 'yan wasa na shida da Maradona ya yi a rayuwarsa. Ya taba horas da kungiyar kwallon kafa ta Argentina na tsawon shekara biyu daga 2008.

Maradona ya sami nasarar kai kungiyar gasar cin kofin duniya da aka yi a Afirka ta Kudu iinda kuma suka kai matsayin daf da na kusa da na karshe.

Kungiyoyin da Diego Maradona ya taba horaswa

  • Textil Mandiyu (Oct 1994 - Dec 1994)
  • Racing Club (Jan 1995 - Mar 1995)
  • Argentina (Oct 2008 - Jul 2010)
  • Al-Wasl (May 2011 - Jul 2012)
  • Al-Fujairah SC (May 2017 - Apr 2018)
  • Dorados (Sep 2018 - Jun 2019)