An yi wa Diego Maradona tiyata

Likitoci sun yi wa Maradona gargadi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Likitoci sun yi wa Maradona gargadi.
An wallafa

An sallami tsohon zakaran kwallon kafar Argentina, Diego Maradona, daga wani asibitin kasar Venezuela bayan an yi masa tiyata a hanji.

Likitoci sun gargade shi cewa nauyin da yake da shi ya zarta ka'ida.

An taba yi wa Maradona, wanda ke da shekaru 55 a duniya, irin wannan tiyata shekaru goma da suka wuce, kuma tun daga wancan lokacin ya kara nauyi, lamarin da ke barazana da lafiyarsa.

Maradona ya tamaka wa Argentina wajen lashe gasar cin kofin kwallon kafar duniya a shekarar 1986.