Barca ta bayyana lambobin rigunan 'yan wasa

Asalin hoton, Getty Images
Bayan da aka kammala cin kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa ta Turai ranar 2 ga watan Satumba, Barcelona ta bayyana lambobin rigunan da 'yan wasanta za su saka mata a bana.
Yawan cin 'yan kwallon za su ci gaba da amfani da lambobinsu kamar kakar bara, sai dai Carles Alena zai sa riga mai lamba 19, yayin da Frenkie de Jong zai sa riga mai lamba 21.
Mai tsaron raga Neto zai yi amfani da riga mai lamba 13 wadda Jasper Cillessen ya yi amfani da ita ya kuma bar Nou Camp.
Antoine Griezman zai sa riga mai lamba 17 wadda Jeison Murilla ya yi amfani da ita, haka kuma lamba 24 da Thomas Vermaelen wanda baya kungiyar yanzu an bai wa Junior ita.
Shi kuwa dan wasa Moussa Wague ya samu ci gaba daga karamar kungiyar zuwa Barca, an kuma damka masa riga mai lamba 16.
Kungiyar ta Barcelona ta ajiye wasu lambobi don kar ta kwana da suka hada da lamba bakwai da 12 da kuma 14.
Lambobin da suke da tarihi a Barcelona sun hada da lamba 10 ta Lionel Messi da ta Gerrard Pique wato lamba uku suna nan kamar yadda suka saba sakawa.
Jordi Alba zai ci gaba da sa riga mai lambar 18 kuma kaka ta takwas kenan da zai yi amfani da ita, sai Ter Stegen da zai ci gaba da sa riga mai lamba 1.
Rakitic na nan da riga mai lamba hudu haka ma Sergio da riga mai lamba biyar da Suarez da zai ci gaba da riga mai lamba tara da kuma Sergi Roberto da zai yi amfani da lamba 20 karo na shida kenan.











