David Luiz ya ce buri ne dalilin komawarsa Arsenal

An wallafa

Dan wasan baya David Luiz ya ce dalilin da ya sa ya bar Chelsea ya koma Arsenal saboda burinsa kuma saboda yana son fuskantar sabon kalubale.

Dan wasan mai shekara 32 ya fara haskawa ranar Asabar a wasan da Arsenal ta doke Burnley 2-1 bayan komawa taka leda a kungiyar a ranar da aka rufe kasuwar musayar 'yan wasa.

Chelsea da ta doke Arsenal a wasan karshe na lashe kofin Europa, ita ce ta zo matsayi na uku a kakar da ta gabata, yayin da Arsenal ta kasance matsayi na biyar.

Amma David Luiz ya ce shi mutum ne mai buri, kuma shi ne dalilin da ya sa ya koma Arsenal. "Ina son fuskantar wani sabon kalubale," in ji shi.

Sai dai ana ganin sabon Kocin Chelsea Frank Lampard ne ya sa dan wasan komawa Arsenal bayan ya shaida masa cewa ba zai dinga fara wasa da shi ba, duk da dan wasan na Brazil ya lashe kofi shida a Chelsea.

Ana sa ran Kocin Arsenal Unai Emery zai hada Luiz da Sokratis Papastathopoulos yayin da Arsenal ta samu nasara a wasanni biyun da ta buga na farko a Premier.