Zaha ya nace sai ya bar Palace, abin da yana Dybala komawa Spurs

An wallafa

Wilfried Zaha ya sha mamaki bayan da aka rufe kasuwar saye da musayar 'yan wasa a Ingila a jiya Alhamis, inda ya kasa koma wa Everton. Sai dai duk da haka dan wasan mai shekara 26 ya hakikance cewa sai ya bar Crystal Palace, a cewar rahoton Telegraph.

Ita kuwa jaridar Mail cewa ta yi dan wasan na Ivory Coast yana fargabar cewa barinsa kulob din zai yi wuya bayan rufe kasuwar a Ingila.

Har wa yau, Mirror ta ruwaito cewa kocin Crystal Palace Roy Hodgson ya sallami Zaha daga filin atasaye saboda "zuciyarsa ba ta kulob din" bayan dan wasan ya mika takardar bukatar barin kulob din ranar Laraba.

Kazalika, jaridar Sun ta ruwaito cewa Chelsea za ta mika tayin fan miliyan 80 domin daukar Zaha a watan Janairu mai zuwa idan har sun yi sa'a an cire masu takunkumin sayen 'yan wasa da ke kansu a yanzu.

Kafar talabijin ta ESPN kuwa cewa ta yi, an kasa cimma matsaya ne kan hakkin mallakar hotunan talla na Paulo Dybala tsakanin Tottenhnam da Juventus, abin da ya hana komawar dan wasan zuwa Tottenham.

A rahoton 90min kuwa, Tottenham ta nemi taimakon Juventus ne kan hakkin mallakar hotunan, tallafin da Juventus din ba ta shirya bayarwa ba.

Tottenham din ta yi tsammanin cewa sun cimma yarjejeniyar fan miliyan 64 kan Dybala amma sai Juve ta janye sha'awarta ta sayar da dan kwallon biyo bayan komawar Lukaku Inter Milan daga Man United, in ji Telegraph.

Real Madrid ta yi imanin cewa ta rasa damar daukar Pogba ganin cewa Manchester United ba ta dauki wani madadinsa ba kafin rufe kasuwar sayen 'yan wasa a jiya Alhamis.

Marca ta ruwaito cewa sakamakon haka, yanzu Madrid za ta mayar da hankali kan daukar Neymar mai shekara 27 daga PSG.