Dani Ceballos: Arsenal ta aminci ta karbi aron dan wasan Real Madrid

    • Marubuci, Daga David Ornstein
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
  • An wallafa

Arsenal ta cimma yarjejeniyar daukar aron dan wasan tsakiya na Real Madrid kuma dan Spaniya Dani Ceballos, domin taka mata leda a kakar 2019-20.

Ceballos, mai shekara 22, ya yi wa Real wasa sau 56 tun da ya koma can a shekara ta 2017, amma kuma ana ta baza jita-jitar tafiyarsa Arsenal da Tottenham a bana.

Ana sa ran tsohon dan wasan na Real Betis ya cike gurbin da Aaron Ramsey, wanda ya koma Juventus, ya bari.

Haka kuma Arsenal din na shirin sayen dan wasan baya na Saint-Etienne William Saliba, mai shekara 18.

Za a sayi matashin dan wasan na tawagar Faransa kusan fam miliyan 27, kuma zai koma Saint-Etienne aro a kaka ta gaba, kafin ya koma Arsenal din a 2020.

Saliba ya bayyana sha'awarsa ta tafiya Arsenal duk da cewa daga karshen nan Tottenham, ta nuna bukatar sayensa.