An sassaka mutum-mutumin Melania Trump

An wallafa

An yi wani mutum-mutumin uwargidan Shugaban Amurka Melania Trump wanda aka girke a wajen garin Sevnica da ke kasarta ta asali wato Slovenia.

An dai sassaka wani icce ne inda aka mayar da shi mutum-mutimi kuma yana siffanta Misis Trump sanye da shudin kaya tana daga hannu.

Sai dai wannan mutum-mutumi ya jawo sharhi daban-daban inda wasu ke cewa an siffanta Melania Trump tamkar dodaniya da za ta rinka tsorata mutane.

Amma wanda ya sassaka mutum-mutumin wato Brad Downey ya ce duk da irin sukar da ake yi, ya tabbatar da cewa abin da ya sassaka ya yi kyau kuma na isar da sako.

Wata mazauniyar garin na Sevnica Katrina mai shekaru 66, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wannan mutum-mutumin babban ci gaba ne ga kasar ta Slovenia kuma Misis Trump ta zama gwarzuwa a Amurka tunda ita ce kololuwa a mata a halin yanzu a Amurka.

Misis Melania ta auri Trump a 2005 kuma ita ce uwar gidan shugaban Amurka ta biyu wacce ba asalin 'yar Amurka ba.

Garin Sevnica dai ya zamo wurin yawon bude ido tun bayan da mijin Melania wato Donald Trump ya zamo shugaban Amurka a 2017.