Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Melania Trump ta isa Malawi da Kenya
To a cigaba da ziyarar da uwargidan shugaban Amurka ke yi a nahiyar Afirka, Melania Trump ta isa kasar Malawi, kasa ta biyu cikin jerin kasashe hudu da za ta ziyarta.
A Malawin, ana sa ran Misis Trump ta mayar da hankali ne kan batutuwan inganta rayukan kananan yara a daidai lokacin da gwamnatin Amurka da maigidanta ke jagoranta ke kokarin rage yawan tallafin da take ba kasashen Afirka.
Misis Trump ta fara ziyarar ta ta ne a wata makarantar firamare da ke Lilongwe, babban birnin kasar ta Malawi, inda matar shugaban kasar Gertrude Mutharika ta raka ta.
Kafin wannan ziyarar, Misis Trump ta ce tana son ganin hanyoyin da Amurka za ta cigaba da taimaka wa Malawin ta bangaren bayar da tallafi ga shirinta na inganta ilimin kananan yara.
Gwamnatin maigidanta ba ta da farin jini a Malawi, kuma wasu 'yan kasar sun yi zanga-zangar nuna kin amincewa da zuwan uwargidansa kasar, cikinsu akwai wasu Amurkawa masu adawa da salon mulkin Mista Trump.
A halin da ake ciki, Misis Trump ta bar Malawi zuwa Kenya, kasa ta uku a cikin jerin kasashen da za ta ziyarta.