Arsenal za ta sayar da Ozil, Chelsea za ta dauki Lampard

An wallafa

Chelsea za ta nada Frank Lampard a matsayin sabon kocinta bayan Maurizio Sarri ya yi watsi da tayin ci gaba da aikinsa.

Lampard da ke horar da Derby ya ce yana son Didier Drogba ya kasance cikin mataimakansa, maimakon John Terry. (Sun)

Dan wasan tsakiya na Brazil Willian mai shekara 30, yana da dab da sabunta kwantaraginsa a Chelsea. (Sun)

Arsenal ta sa Mesut Ozil kasuwa domin samun kudaden da za ta sayo sabbin 'yan wasa. (Mirror)

Arsenal na shirin karawa dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 29 albashi, saboda farautarsa da ake yi a China. (Mirror)

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce yana iya sayar da Mohamed Salah na Masar idan har dan wasan da yake farauta Nicolas Pepe na Ivory Coast da ke taka leda a Lille ya amince ya dawo Anfield. (Le10 Sport - in French)

Dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekatra 26, ya nace kan cewa yana son ya bar Old Trafford zuwa Real Madrid. (Marca)

Manchester United na shirin karawa golanta avid de Gea, mai shekara 28 albashi don kada ya bar Old Trafford inda kwangilarsa ta kawo karshe a mayun 2020. (ESPN)