Sadio Mane zai kafa tarihi a Camp Nou

Asalin hoton, Getty Images
Sadio Mane zai kafa tarihi a Spaniya da zarar ya ci Barcelona kwallo a wasan Champions League karawar daf da karshe da Liverpool karawar daf ranar Laraba.
Mane dan kwallon tawagar Senegal, ya ci kwallo 24 a kakar bana, kuma da zarar ya kara a Camp Nou zai yi kan-kan-kan da Mohamed Salah wanda keda 25 kawo yanzu.
Hakan zai zama karon farko da 'yan Liverpool biyu za su ci kwallaye 25 ko fiye da haka a kakar tamaula daya.
A kakar bara ne Mohamed Salah ya ci kwallo 44, shi kuwa dan wasan tawagar Brazil, Roberto Firmino guda 25 ya zura a raga.
Mane ya ci kwallo a kalla daya a kowanne wasa tun daga na cikin rukuni tun lokacin da ya koma Anfield a 2016.
Hakan ya hada da guda tara da ya ci a wasa 10, ya kuma ci kwallo a wasan karshe a Kiev da Real Madrid.
Mane ya buga wa Liverpool wasa 45 a kara bana ya kuma ci kwallo 24, inda ya zura 20 a raga a gasar Premier.







