Arsenal da Liverpool na son karbo Dembele

An wallafa

Kungiyar Arsenal tana son karbo dan wasan Barcelona Ousmane Dembele - Sai dai Lionel Messi ya ce Barcelona na bukatar dan wasanta, in ji (Football.London).

Kalaman Messi sun sanyaya wa Arsenal kwarin guiwar zarafin karbo dan wasan.

Kaftin din na Barcelona ya ce tawagarsa na jin dadin yadda Dambele ke taka leda kamar yadda Messi ya shaidawa mundodeportivo.

"Muna bukatar Dembele," in ji Messi.

Liverpool ma tana cikin kungiyoyin Ingila da ke sha'awar karbo Dambele, idan har za ta iya biyan kudaden da Barcelona za ta bukata, in ji (El Confidencial, via Star).

Dan wasan ma Faransa, wanda aka alakanta shi da kungiyar Arsenal, na fuskantar matsaloli game da zamansa a Barcelona, bayan nuna damuwa kan yadda ake ajiye shi da benci.

Ana tunanin Arsenal za ta bukaci sayen Dambele a watan Janairu domin maye Danny Welbeck da zai kwashe kakar bana ba tare da ya dawo wasa ba, sanadiyar raunin da ya samu a wasan Arsenal da Sporting ta Portugal a Europa league.

Rahotanni daga ingila sun nuna cewa har magoya bayan Arsenal sun fara nuna sha'awar suna son a karbo Dembele.

Sai dai yanzu akwai alamun an fara yabonsa a Spain, bayan burgewar da ya yi a karawar Barcelona da Espanyol ranar Asabar, inda ya samu yabo daga Messi, wanda ya ce Barcelona na bukatarsa.