Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pochetino na dari-darin haduwa da Barcelona
Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino ya ja kunnen 'yan wasan sa cewar Barcelona ba za ta yi musu sako-sako ba, idan suka hadu a gasar cin kofin Zakarun Turai a ranar Talata.
Tottenham ta samu karfin gwiwar zuwa Spaniya, bayan da ta doke Leicester City da ci 2-0 a ranar Asabar a gasar Premier wasan mako na 16.
Kungiyar ta Ingila ita ce ta biyu a rukuni na biyu a gasar ta Zakarun Turai da maki bakwai daidai da na Inter Milan, saboda haka da zarar ta ci Barcelona za ta kai wasan zagaye na biyu kenan.
Ita kuwa Inter Milan wadda za ta kece raini da PSV mai maki daya kacal a ranar ta Talata, tana sa ran a doke Tottenham a Spaniya, ita kuma ta ci wasanta ta kai zagayen gaba a gasar.
Pochetino ya ce za su fuskanci kalubale kuma duk da Barcelona ta kai zagaye na biyu, a gasar Zakarun Turai babu batun daga kafa.