Macron na son Najeriya ta goyi bayan Faransa a Rasha

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya nemi 'yan Najeriya su goyi bayan kasarsa a gasar kofin duniyar da ake yi a Rasha.

Shugaban ya yi wannan maganar ne a lokacin da ya kai ziyara Najeriya.

Macron ya ce "tun da dai Najeriya ta fice daga gasar kamata ya yi 'yan kasar su mara wa kasarsa baya."

Wakilin sashen wasanni na BBC, Nick Cavell, ya ce 13 daga cikin 'yan wasan dake tawagar Faransa za su iya taka wa wata kasar Afirka leda.

Dan uwan Paul Pogba, Florentin, yana buga wa Guinea ( ya kuma buga wa 'yan kasa da shekara 20 na Faransa wasa)

Dan uwan Steve Mandanda, Parfait, yana buga wa Jamhuriyar Dimkradiyyar Kongo wasa (kuma ya buga wa tawagar 'yan kasa da shekara 21 ta Faransa wasa).

A wasanta na gaba, Faransa za ta kara ne da Uruguay ranar Juma'a zagayen kusa da dab da karshe.