Dubban mutane na son a hukunta Sergio Ramos kan Mo Salah

Mo Salah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mo Salah ya fita daga fili yana kuka bayan raunin da ya samu
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ana cigaba da nuna goyon baya ga wata takardar kara ta intanet da ke neman a hukunta Sergio Ramos kan cewar ya ji wa Mohamed Salah ciwo da gangan.

An kai karar Sergio Ramos kan cewar da gangan ya yi wa Mo Salah keta a wasan karshe na gasar zakarun Turai da aka buga tsakanin Real Madrid da Liverpool.

Kuma a lokacin da ake wallafa wannan labarin mutum 500,000 ne suka nuna goyon baya ga karar da ke neman a hukunta Ramos da aka wallafa a shafin koke na intanet, petition.org.

Kawo yanzu dai hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa, da ake naman ta hukunta Ramos ba ta ce komai game da karar ba.

Tun ranar da lamarin ya faru ne dai Sergio Ramos ya yi wa Mohamed Salah fatan samun sauki da wuri.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Ramos ya yi wa Salah fatan alkhairi.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Shi kuma Mohamed Salah ya ce yana fatan cewa zai samu buga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a watan gobe.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, dan wasan na Masar da ke taka leda a Liverpool, ya gode wa masoyansa a fadin duniya, yana mai shan alwashin burge su.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2