Steven Gerrard ya zama sabon kocin Rangers

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Kungiyar Rangers ta Scotland ta nada Steven Gerrard a matsayin sabon kocinta.
Tsohon kaftin din na Liverpool ya amince da yarjejeniyar shekara hudu da kungiyar.
Gerrard zai fara aikin horar da Rangers ne a kaka mai kamawa.
Tsohon dan wasan na Ingila mai shekaru 37 ya yi alkawarin kayatar da magoya bayan Rangers.
Gerrard ya zabi tsohon kafin din Scotland Gary McAllister a matsayin wanda zai taimaka ma sa a aikin horar da kungiyar.
Steven Gerrard ya lashe kofuna tara a wasanni 710 da ya bugawa Liverpool a shekara 19, sannan ya buga wa Ingila wasa 114.
A 2016 ne ya yi ritaya daga tamaula bayan ya koma LA Galaxy a Amurka.
Gerrard yanzu ya gaji Graeme Murty ne da Rangers ta ba rikon kwarya.











