Moses ya kai Najeriya ga nasara, kamar yadda Morocco da Tunisia suka yi

Moses

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar Juma'a Najeriya ta doke Poland da ci 1-0 a wasan tunkarar gasar cin kofin duniya inda dan wasan Chelsea Victor Moses ya samar mata fanaretin, bayan da aka yi masa keta, ya kuma buga ya ci.

Su ma kasashen Afirka biyu sun yi nasara inda Tunisia ta doke Iran da ci 1-0 yayin da Morocco ta buge Serbia da ci 2-1.

A bangare guda, Senegal ta da Uzbekistan sun tashi da ci 1-1, yayin da Masar ta sha kashi a hannun Portugal da ci 2-1.

Kwallon da Moses ya samar wa Najeriya za ta kara wa kasar kuzari, inda tawagar da ta doke ke matsayi na shida a duniya, wato tana gaba da Super Eagles da matsayi 46.

Wannan ne karo na biyu da Super Eagles suka yi bajinta bayan kashi da suka bai wa Argentina da ci 4-2 a shekarar da ta wuce.

Najeriya za ta fafata da Argentina da Croatia da kuma Iceland a wasan rukuni-rukuni na gasar cin kofin duniya da za a yi a Russia.

Boutaib

Asalin hoton, Getty Images

Ita ma Morocco ta ci nata wasan a Turai inda dan wasanta Khalid Boutaib ya ci kwallon da ta ba su nasara a minti na 40 suka tashi da ci 2-1 da Serbia a birnin Turin na Italiya.

Fanaretin da Hakim Ziyech ya buga ne ya sanya kungiyar Atlas Lions a gaba, sai dai Dusan Tadic ya farke wa Serbia kwallon, ko da yake ba su cancanci zuwa Russia ba.

Tunisia ta ba da damar buga wasa karon farko ga 'yan wasa uku na kasar haifaffun Faransa - Ellyes Skhiri, Yohan Benalouane da Seif-Eddine Khaoui - inda ta doke Iran 1-0 a Rades.

'Yan wasan sun cancanci buga wa kasar wasa saboda iyayensu 'yan asalin Tunisia ne kuma jami'ai sun yi raddi ga sukar da aka yi cewa "tsuna baza komarsu domin tabbatar da cewa sun yi nasarar zuwa gasar cin kofin kwallon kafar duniya".