Ousmane Dembele zai yi jinyar mako hudu

Barcelona

Asalin hoton, Barcelona FC

Bayanan hoto, Karo na biyu kenan da Dembele ke jin rauni tun komawarsa Barcelona
An wallafa

Dan wasan Barcelona wanda ta saya mafi tsada a tarihi, Ousmane Dembele zai yi jinyar mako uku zuwa wata daya.

Dan kwallon ya ji rauni ne a karawar da Barcelona ta doke Real Sociedad 4-2 a wasan gasar La Liga da suka kara a ranar Lahadi.

Tun farko an yi fargabar cewar ya fama raunin da ya warke daga jinya ne kwanan nan, amma da likitoci suka auna sai suka ce sabon rauni ya yi.

Dembele wanda Barca ta sayo daga Borrussia Dortmund kan fam miliyan 135.5 ya dawo ne daga raunin da ya yi jinyar wata hudu a mako biyu da suka wuce.

Dan wasan ya yi raunin farko ne a cikin watan Satumba a karawar da Barcelo ta ci Getafe 2-1 a gasar La Liga a ranar Asabar.