Klopp bai jagoranci atisayen Liverpool ba

Jurgen Klopp

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Klopp ya fara jan ragamar Liverpool tun Oktoban 2015
An wallafa

Kungiyar Liverpool ta sanar da cewar kocinta Jurgen Kloop bai ja ragamar atisaye ba a ranar Laraba, bayan da aka kai shi asibiti sakamakon rashin lafiya.

Likitoci sun duba Kloop mai shekara 50, domin tabbatar da cewar lafiyarsa kalau a matakin riga kafi.

Liverpool ta ce a yammacin Laraba zai koma gida, idan likitocin sun tabbatar da koshin lafiyar kocin.

Sai dai kuma Klopp zai bukaci a ci gaba da duba koshin lafiyarsa lokaci-lokaci.

Liverpool tana ta biyar a kan teburin Premier za kuma ta kara da Southampton a ranar Asabar a gasar Premier a Anfield.