Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta dauki kofi bayan doke Man United 2-1
Real Madrid ta sake rike kofin zakaran zakaru na Turai, Super Cup, bayan da ta doke Manchester United da ci 2-1 a wasan da ta mamaye su a babban birnin Macedonia, Skopje, cikin tsananin zafi.
Casemiro ne ya fara daga raga a minti na 24 bayan da Dani Carvajal ya sako kwallo tsakanin 'yan bayan United din.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a minti na 52 sai Isco, ya tura wa Gareth Bale kwallo, shi ma ya mayar masa, a wani ba-ni-in-ba-ka suka yi, dan Spaniyar ya sheka ta biyu a raga.
Romelu Lukaku, wanda ya barar da wata dama, bayan golan Madrid ya yi aman harin da Pogba ya kai da ka can a minti na 54, bayan minti bakwai tsakani ya natsu ya sheka daya a raga bayan wani aman da Keylor Navas din ya sake yi.
Idan dai ba a manta ba kwana 16 da ya wuce kungiyoyin biyu suka kara a Santa Clara, Amurka, inda suka tashi 11, amma kuma United ta yi nasara a bugun fanareti.
Jose Mourinho bai taba doke Real Madrid a wata gasa ba, inda ya yi canjaras daya, ya yi rashin nasara sau hudu a karawa biyar.