Amfanin tsufa

Yawancinmu muna tsoron tsufa. Amma yanzu akwai tarin shedun da ke nuna cewa tsufa yana kawo farin ciki da basira har ma da karin jin dadin saduwa.
Zaria Gorvett ta yi mana nazari
''Tsufa abu ne mai kyau, idan ka yi la'akari da daya zabin'' kamar yadda 'yan magana ke cewa. Ko kuma in ce ''kuruci dangin hauka''
Barka da zuwa shekarar tsufa. Duniya na shirin tunkarar kalubalen da za ta gamu da su na tattalin arziki da zamantakewa, domin sama da mutane miliyan 800 ne suka kai sama da shekara 60 ga kuma wasu da suka kai ko suka haura shekara 100, da suka zarta yawan al'ummar Iceland gaba daya ( kusan 329,000).
Kama daga cutuka da tattarewa da sakin fata da kuma rasawa ko raguwar wasu muhimman ayyukan jiki (gani da ji da jin kanshi ko wari da tafiya da sauransu), tsufa na tattare da gazawa iri-iri da jiyya da kuma kasa cimma bukata. To ko akwai wani kyakkyawan fata ko haske ga wadanda suka kan hanyarsu ta shiga wannan rukuni na rayuwa?
Tun a lokacin da ana danganta tsufa da tabarbarewa ko lalacewar jiki. Mutanen Girka suna da yadda suke daukar tsufa, inda da yawa daga cikinsu suke kallon tsufan kansa a matsayin cuta.
To amma binciken kimiyya na baya-bayan nan ya nuna cewa tsufa dai ba tabarbarewa ko koma baya ba ne na kai tsaye kamar yadda ake dauka.
Kamar yadda a wasu bayanai da wannan sashe na rubuce-rubuce na BBC ya yi a baya, ya nuna rayuwa na kaiwa koli-koli can gaba da lokacin da kake tunani.

Asalin hoton, Thinkstock
Daga wane lokaci ne shekarun tsufa ke farawa?
Mawakin nan Dante yana ganin shekarun tsufa sun fara ne daga 45. Wani bincike na ra'ayin jama'a da aka yi a Birtaniya ya nuna cewa suna kamawa ne daga shekara 59 kamar yadda mutanen suke gani.
Hakka dai abin yake yawan shekarun mai bayyana ra'ayinsa yawan shekarun da yake bayyanawa a matsayin na tsufa.
Idan mutum yana da shekaru da yawa sai ya ambaci wasu shekaru mai yawa ya ce su ne na tsufa.
To amma Majalisar dinkin duniya da yawancin masana kimiyya sun ayyana duk shekarar da ta wuce 60 ne, daga nan tsufa ke farawa.
'Yan larurori
Ba kwakwalwa ba ce kadai take samun wayewa da ilimi yayin da mutum yake shekaru.
Garkuwar jikin mutum tana gamuwa da miliyoyin abubuwan da za su iya zama hadari a gare ta a kullum.
A matsayin garkuwar na 'yar sandar jiki ko mai kare lafiyar jiki, tana bukatar sanin yadda za ta iya gane duk wata barazana ko hadari.
A kan haka ne jikinmu yake samar da sinadari (white blood cell) da yake tsarawa ya yi kama da miliyoyin masu yi wa jikinmu kutse ta yadda zai iya yakarsu.
Da zarar wadannan sinadarai sun gane abokin gaba sai su tsaya kusa, su gane shi da kyau, su haddace yadda kamanninsa yake.Nan gaba da ya zo sai su tashi tsaye, su yake shi ba tare da wani bata lokaci ba.

Asalin hoton, science photo library
John Upham na jami'ar Queensland da ke Australia ya ce wannan hadda ke gane kwayar cuta da garkuwar jiki ke yi na dadewa sosai (ba ta manta wa).
''Mutanen da suka gamu da annoba daban-daban, garkuwar jikinsu na iya tuna kwayoyin cuta har tsawon shekaru 40 zuwa 50 a wani lokacin.
Amma idan mutum ya kai shekara 70 ko 80 sai garkuwar ta fara mantawa da yadda kwayoyin cutar su ke.
Amma dai a sani daga shekara 40 har zuwa 60 zuwa farkon 70 da wani abu, garkuwar tana iya tuna kwayoyin cuta.'' kamar yadda masanin ya yi bayani.
Wannan kwarewar kariya da jikin mutumin yake da ita, na nufin zai iya gamuwa da 'yan matsaloli ne kadan.
Yayin da dan shekara 20 ake ganin zai iya gamuwa da matsaloli biyu ko uku na lfaiya a shekara daya, wanda ya kai shekara 50 da wani abu ya kan gamu da larura yawanci daya ko biyu ne kawai a shekara.
Sai dai wasu ayyukan na garkuwar jiki sukan yi rauni yayin da mutum yake girma ko kara shekaru.
Jikin yana samar da sinadarai (white blodd cells) mausu yakar kwayoyin cuta ne kadan a wannan lokaci kuma sai su zama marassa kuzari.
Haka kuma kwayoyin da suke gane abokin gabar jiki su yake shi su ma a wannan lokaci na yawan shekaru sai su ragu. To amma ina laifi idan hakan zai ceci rayuwa ne?
Tsallake annoba
Annobar masassar da aka yi a 1918 ita ce mafi hadari a tarihin dan adam, inda ta hallaka mutane miliyan 50.
Amma kuma ta fi shafar rukunin mutanen da ake ganin su ne masu karfi da kuruciya da suka kama daga shekara 20 zuwa 40.
Haka ita ma annobar masassar alade da aka yi a shekara ta 2009 ta bi irin wannan salo ne na halaka mutanen da yawanci suke kasa da shekara 65.

Asalin hoton, Science Photo Library
Ana ganin kwayoyin cutar suna sa garkuwar jikin wanda ta kama ta wuce gona da iri wajen yaki da kwayoyin.
Saboda jikin mutanen da suke da garkuwar jiki mafi karfi yana daukar mataki ne na yaki na ba sani ba sabo wanda har yakan kai ga yi wa jiki illa.
Ita kuwa garkuwar jiki mai kyau tana mayar da martani ne kan bayanan da ta samu masu kyau a duk lokacin da aka gano wata kwayar cyta a jiki, inda jijiyoyi da kwayoyin halittar kusa da wurin da kwayar cutar take, za su aika da sakon neman taimako.
Daga nan sai jiki ya turo kwayoyin yaki da cutar, ya kuma cigaba da kara turo su.
To amma a wani lokacin sai abin ya wuce yadda ake bukata, har kwayoyin da suke zuwa domin wannan yaki, su rika kama kwayoyin halittu masu amfani suna kashewa, har abin ya zama wata illa kuma.
Ya zuwa yanzu ba a san abin da yake sa a samu wannan yanayi da mayakan suke zuwa fiye da kima ba.
Amma wani bincike da ake yi yanzu ya sa an bullo da wata hanya ta yin maganin masassar, wanda zai mayar da hankali kan magance hauhawar zuwan sojojin da ke yakin cutar maimakon kwayar cutar kanta.
Gushewar kan-jiki
Akwai kuma kyakkyawan albishir ga mutanen da suke da kan-jiki su ma.
Duk da cewa har yanzu ana muhawara mai zafi kan ainahin abin da ke haddasa kan-jiki, ana ganin duka dai kwayoyin yaki da cuta na jiki ne ke haddasawa.
Kwayar da ake zargi da laifin (immunoglobulin E) da sauran dakarun jiki masu yaki da cutuka, yawan samar da su na raguwa yayin mutum yake tsufa.
Mitchell Grayson na asibitin yara na Winsconsin a Amurka, ya ce, yayin da kake kara girma tsananin alamun kan-jikin na raguwa.
''Cutukan kan-jiki suna yawa ne a lokacin da mutum yake yaro, sannan kuma sai su rika raguwa yayin da mutum ya kai shekarun balaga har zuwa sama da shekara 20.
Idan kuma mutum ya kai shekara 30 zuwa gaba sai cutukan su sake tasowa, har sai mutum ya kai shekara hamsin zuwa sama ko sittin zuwa gaba, a lokacin ne kuma cutukan za su yi sauki.
Karin wayo
Babu karancin kalmomin da za a iya bayyana illolin da tsufa ke yi wa kwakwalwa. Amma duk da haka a fannin wasu muhimman ayyuka ana ganin kwakwalwar da ta tsufa ta fi basira da wayo.

Asalin hoton, Science Photo Library
Micheal Ramscar na jami'ar Tubingen da ke Jamus, ya ce mun yi wa yadda kwakwalwa ke tsufa mummunar fahimta.
''Yawan kwayoyin halittar da ke aikin kai sakon motsi (neurons) wadanda ke cikin kwakwalwar mutum suna kai karshen yawansu ne a kusan sati 28 bayan haihuwa, amma kusan rabin yawansu suna mutuwa zuwa karshen lokacin balaga.
Tun da yawanci ba ma daukar lokacin da ya kama daga haihuwa zuwa shekara 18 a matsayin lokacin dusashewa (raguwa), za mu iya cewa kenan girman kwakwalwa na yawan kwayoyin halittar kai sakon motsi (neuron) da ke cikinta ba wata alama ba ce ta wani abu.''
A wani nazari (Seattle Longitudinal Study), an bi diddigin kaifin kwakwalwar wasu mutane 6,000 tun shekarar 1956, wanda wannan shi ne nazari na mafi tsawon lokaci da aka taba yi irinsa, da rukunin mutane daya wadanda ake gwaji a kansu duk shekara bakwai.
Abin da aka gano daga nazarin shi ne, yayin da manya daga cikinsu ba su da kokari a lissafi kuma suna da nawa (jinkiri) wajen bin umarni, amma a bangaren sanin kalmomi da haddar wani abu da aka fada musu da baki da dabarar magance wata matsala da kuma gane hanyar zuwa wani wuri sun fi kokari a dukkanin wadannan fannoni a shekarunsu na sama da 40 da kuma sama da 50, idan aka kwatanta da lokacin da suke shekaru 20 zuwa sama.
Gary Small wanda ke nazarin illolin da suka shafi hankalin mutum sakamakon shekaru, a jami'ar California, ya ce wannan duka albarkacin ilimin da mutun ya tara ne tsawon karin shekarun da ya yi.
''Mutane suna sanin abin da yake da muhimmanci da iya shawo kan matsala bayan shekaru na koyo. Sannan kuma akwai taruwar wani nau'i na ilimi daban-daban, abin da ake kira tarin basira.''
Jima'i mafi gamsarwa
Nazarce-nazarce sun nuna cewa mutanen da suka fi shekaru suna jima'i sosai kuma mai gamsarwa fiye da yadda kake tunani.
Wani nazari da aka yi kan jima'i da gamusawar da mata a lokacin da suka kai shekara 80 zuwa sama ya gano cewa rabinsu suna yin inzali a duk lokacin da aka sadu da su ko kuma a yawancin lokaci.
Wadansu bincike-binciken ma sun gano irin wannan bayani, inda a wani bincike a kan mutanen da suka wuce shekara 60, aka gano kashi 74 cikin dari na maza da kuma kashi 70 cikin dari na mata, suna samun biyan bukata da gamsuwa a jima' fiye da yadda suke samu a lokacin suna shekara 40 zuwa sama.
Masaniya kan mu'amullar namiji da mace Tara Saglio, wadda take zaune a Lanadan ta danganta wannan ga cewa matan da suke da shekaru da yawa sun fi sakin jiki da kuma karfin hali na bayyana duk wani abu a game da abin da da ya shafi jima'i ko mu'amullarsu ta saduwa. Wannan kwarin gwiwa shi ne ke sa su ji dadin jima'i sosai.''

Asalin hoton, Science Photo Library
Karancin ciwon kai
Irin ciwon kan nan na bari daya da mutum yakan yi fama da shi, yana raguwa yayin da mutum yake kara shekaru.
Wani bincike da aka yi a Sweden a kan masu fama da ciwon, 'yan shekara 18 zuwa sama, ya gano cewa ciwon na rage yawan tasowa da rashin tsanani kuma na dan lokaci kadan yayin da mutum ke kara shekaru.
Daga cikin mutane 374 da aka yi binciken a kansu hudu ne kawai ciwon ya tsananta da suke girma.
Rage yawan gumi
Yayin da mutane suke tsufa hanyoyin da suke kawo gumi suna tsukewa da raguwa. Bincike ya nuna 'yan shekara 20 zuwa sama na yin gumi fiye da wadanda suka kai shekara 50 zuwa sama da kuma wadanda suke dan zarta shekara 60.
Bijire wa mutuwa
Har yanzu ba ka yarda ba?
Duk da cewa ka kai shekarun tsufa ka da ka dauka mutuwa na gab da kai. Ba haka lamarin yake ba.
Tsoffin da suka fi tsufa sun fi lafiya fiye da da kuma har yanzu suna da damar yin karin bikin ranakun haihuwarsu na 'yan shekaru.
A 2011 zuwa 2014, yawancin mutanen da suke shekara 25 suna da damar rayuwa har zuwa shekara 84 ga mata, yayin da su kuma maza za su iya kaiwa 80.
Su kuwa masu shekara 95 za su iya sa ran ganin shekararsu ta 98 ga mata kenan yayin da maza za su iya ganin ta 97.
Hatta a shekara 80 mata suna da dama kashi 95 cikin dari ta kara shekara daya a rayuwarsu.
Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan <link type="page"><caption> The benefits of getting older</caption><url href="http://bbc.com.im/future/story/20151028-the-benefits-of-getting-older%22 platform="highweb"/></link>









