Hikayata 2020: Labarin 'Numfashin Siyasata' da ya zo na biyu

An wallafa

Ku latsa hoton da ke ƙasa don sauraron labarin:

Bayanan sautiHikayata 2020: Labarin ‘Numfashin Siyasata’ da ya zo na biyu

Wannan labarin hakkin mallakar BBC ne. Ba a yarda wani ko wata su yi amfani da shi ta ko wane salo ba, ko da yaɗa shi ne ta shafukan sada zumunta. Idan aka yi hakan kuma, to BBC za ta ɗauki mataki har da na shari'a.

Jikina ya ba ni cewa wani al'amari yana daf da aukuwa gare ni, yanayin da ba zan iya tantance daɗinsa ko rashin daɗinsa ba duk da yawan mutuwa da jikina ke yi.

Hakan ba ta sa na yi ƙasa a gwiwa ba a cikin harkokina na yau da kullum.

Babban abin da na sani guda ɗaya shi ne na yi baƙin jini tare da ƙaurin suna a wannan karkara tamu.

Gungun samari ne suka biyo ni cikin dare bayan na duro daga katangar gidanmu ta bayan gida sakamakon wutar da suka cinna wa gidan.

"Ga ta can ta dira ta baya ku kama ta" na ji ɗaya daga cikin su ya faɗa.

Jin haka bai ƙara min komai ba illa tsananin buƙatar tserar da raina.

Gudu nake suna bi na duk gidan da na dosa don neman ceto sai a yi biris da ni, don haka na nufi gona da gudu na shige wata gona da wani mai rangwamen hankali ke yawan zama, a daidai wannan lokacin na roƙi Allah Subhana wata ala Ya kawo min ɗauki ba don halina ba sai don aikin alheri da zan yi wa mutanen da nake son wakilta.

Ina shiga cikin duhuwar gonar nan na ji motsin mutum ya yi tari.

Ban yi wata-wata ba na nufi in da yake na rakuɓe a bayansa. Samarin nan na isowa na ji ya ce "Su waye nan, mutane ko aljanu 'yan uwana?" kafin ka ce wani abu tuni sun juya da gudu sun bar gurin.

Nan dai na kasance cikin fargaban abin da bawan Allahn nan zai yi min, amma cikin ikon Allah ko kula ni bai yi ba har gari ya waye.

Cikin rakiyar jami'an tsaron gundumarmu muka nufi gidan iyayena inda na tarar da gidan ya ƙone ƙurmus na kuma rasa iyayena a gobarar da samarin nan suka haddasa.

Ƙwaƙwalwata ta yi rakiyar tunanina zuwa abin da ya gudana a daren jiya tsakanina da iyayena "Asabe ki gudu, Asabe ki ceci rayuwarki" in ji mahaifina wanda hayaƙi ya fara turnuƙe maƙoshinsa, ita kuwa uwata tuni ta suma, na kurma ihun neman ceto amma babu wanda na gani illa ife-ifen matasan nan.

Mahaifina mutum ne mai girman gaske hakan ce ma ta sa na kasa kinkimar sa mu gudu, daɗin daɗawa ma ko da na iya ɗaukar sa ba za mu tsira ba a gurin matasan nan.

Ban iya kallon gawar iyayena ba saboda rashin kyaun gani, kamar an ƙona guma-guman itace.

Wannan layi ne

Zuciyata ta yi birgirmar tashin hankalin abin da ya faru baya kafin aukuwar wannan mummunar al'amari.

Mutanen karkararmu mutane ne da ba sa son sauyi ko wane iri ne, sannan ba su ba wa ilimi muhimmanci ba musamman ilimin 'ya mace.

Don haka babu wani abu na cigaba da yake isa gare mu don ko siyasar ma ba sa yi.

Tun ina ƙarama wani kawuna ya ɗauke ni riƙo a birni, a nan na yi karatun addini da na boko wato na kammala karatun sakandare har aka yi min aure.

Mutuwar mijina wanda ɗan siyasa ne ya zo daidai da mutuwar kawuna don haka ba ni da makawa sai dai na komo ƙauyenmu gurin iyayena da zama.

Bayan wani lokaci kishin al'ummar ƙauyen mu ya turnuƙo ni, na ƙara bincike a kan yadda gwamnati ta mayar da yankinmu aljihun baya saboda ba mu da wakilan da za su tsaya mana mu sami ababen more rayuwa ko ababen tallafin rayuwa.

Ko rijiyar burtsatsai ba mu da ita bare kuma wani abu wai shi ruwan famfo.

Ban yi wata-wata ba na yanke shawarar tsundumawa cikin siyasa don tsayawa takarar kansila abin da jama'ar gari suka yi wa lakabi da babban zunubi mai shirin jawo wa yankin jafa'i, suka sha alwashin shaƙe numfashin siyasa ta.

Ban damu ba don na sami sahalewar iyayena sun amince tare da sanya min albarka.

Sai dai kuma kash, wannan ƙuduri nawa ya gamu da babban tasgaro musamman ma daga matan ƙauyen waɗanda suke ganin tamkar na fito tsirara tsakiyar kasuwa ina rawa.

Wannan layi ne

Abu kamar wasa duk gidan biki ko taro da ka zaga matan gari ba su da wata hira sai ta mace ta fito neman shugabancin al'umar da ko mazan garin ba su nema ba.

Duk in da a ka zauna yin sallah sai tofin Allah Ya tsine ake yi min.

Ni da iyayena muka zama tamkar mujiyoyi a gurin mutane, na sha kyara da tsangwama da tsana.

Wasu ma cewa suke da gangan mahaifina ya tura ni birni don na koyo karuwanci, suna cewa sai mara mafaɗi ke tsunduma harkar siyasa.

Kasancewar mahaifina ya yi zaman birni ya san harkar duniyar siyasa don haka bai damu da tsangwamar su ba.

Wannan ƙarfin hali nawa ya janyo hankalin wasu tsirarun mutane 'yan asalin ƙaramar hukumar mu amma ba 'yan yankin mu ba, mazauna birni ne suka ga lallai na yi namijin ƙokari wajen nemawa yankina cigaba ta fuskar zamani, don haka na sami goyan baya daga wajensu amma ba daga cikin jama'ata ba.

Duk ƙokarin da a ka yi domin a wayar musu da kai ya ci tura, maimakon su saurare mu ma sai dai a yi mana a ture, a bi mu da tsinuwa har da duwatsu.

Ban yi tsammanin cewa 'yan uwana jinsina na mata za su zama manyan maƙiyan tafiyar nan tawa ba, sai da na gana da limamin gari.

Ganin ba sa tare da ni ya sa na nemi haɗin kan manyan garin don a gudu tare a tsira tare.

Limamin garin na fara nema don ya yi kira da jama'a a ba ni dama na nema wa yankinmu 'yanci.

Bayan na gama kwararo masa buƙatata sai ya ce da ni "Asabe na ji batunki amma in ban da abin ki…a ina kika taɓa jin mace ta shugabanci al'umma?" jin haka ya sa na ƙara gyara zama cikin nutsuwa na mayar masa da martani kamar haka "Allah Ya gafarta ba shugabanci nake nema ba, illa wakilci…" ya katse ni da cewa "Dakata Asabe meye marabar dambe da faɗa…wakilci da shugabanci duk ɗaya ne, tunda duk sai mun dogara da ke mace kafin mu ji abin da ya shafi rayuwarmu ko yankin mu".

Ya nuna ni da ɗan yatsa, sannan ya cigaba da magana "Abin da ya fi alfanu shine ki watsar da wannan gingimemen abin da kika ɗauko wa kan ki, domin ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa".

Da ya gama bayani. Na nisa na yi masa tambaya da cewa " Me zai hana savuwar bindiga a ruwa ranka ya daɗe?" ya kada baki ya ce "Saboda ke mace ce , ba za mu zuba ido mu ga-bari mace ta mulke mu ba, ba a taɓa yi ba, ba za kuma mu bari zamani ya gurɓata mana tarbiya ba". Na yi masa godiya na fice.

Kafin na gama tattaunawa da Limamin gari ashe labari ya baibaye ko'ina wai na zo ƙalubalantar Liman akan batun takarata, nan da nan samari suka tare hanyar komawa ta gida kowanne da tsumagiya, ina karyo kwana na ji saukar tsumagiya a gadon bayana shauuuu.

Daga nan ko ta ina duka ya dinga sauka jikina, tun ina ihun neman agaji har na dangana, na kasa magana don mata da yara ne suka fito suna kallo suna dariya tare da shewa.

Sai da na daina motsi sannan suka ƙyale ni.

Farkawa na yi na ga uwata na gasa min jiki hawaye na kwaranya daga idaniyarta.

Ashe dai wannan somin taɓi ne, bayan kwana biyu na ji sauƙi har na fara fita, na sami 'yan jam'iyyarmu na gabatar musu da janyewa ta daga takara domin tsira da raina, ashe ban tsira ba don zuwa gare su ya alamtawa maƙiyana cewa ina kan bakana. Cikin talatainin dare suka zo suka bankawa gidanmu wuta.

Bayan an kau da gawawwakin iyayena, tsananin binkice ya zaƙulo wadanda suke da hannu a wannan aika-aika, ciki har da manyan gari sai na sami gagarumin goyan bayan wasu gungun mutane mazauna birni 'yan asalin karkararmu waɗanda suka ji labarin abinda ya faru da ni, suka sama mini tsaro mai tsanani.

Da lokacin zaɓe ya zo ba wanda ya fito zaɓe a ƙauyen sai mutane 'yan ƙalilan, hakan nan na ci zaɓe don daman babu abokin takara ko hamayya.

Kafin shekara ta zagayo na dinga kawo musu ayyuka na ci gaba da more rayuwa, kan ka ce wani abu sai ga ƙiyayya ta rikiɗe soyayya, matan gari suna amfana da hanyoyin koyon sana'a iri-iri, suna shi min albarka.

Sai dai kash…babu iyayena a duniya bare su ga wannan rana, ranar da suka sadaukar da rayuwarsu don wanzuwarta, ranar farin cikin al'ummata, ranar da gidan su ba ya rabo da matasa don neman ƙarfafa gwiwar neman ilimi.

Da wannan abin da ya faru mutanen ƙauyenmu suka watsar da tunanin cewa sai mace mara mafaɗi ke shiga harkar siyasa suka rungumi sauyi.

Surayya Zakari Yahaya ce ta rubuta wannan labarin kuma ta shigar da shi gasar rubutun gajerun labarai ta BBC, Hikayata.