Yadda gwamnatin Indiya ke amfani da buldoza 'wajen cin zalin Musulmai'

A bulldozer is being used to demolish the illegal structures of the residence of Javed Ahmed, a local leader who was allegedly involved in the recent violent protests against Bharatiya Janata Party (BJP) former spokeswoman Nupur Sharma's

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, The home of political activist Javed Mohammad was turned into rubble on the orders of the government
    • Marubuci, Daga Geeta Pandey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
  • An wallafa

Buldoza da aka samar shekaru 100 da suka gabata, ana amfani da ita a sassan duniya wajen gine-ginen gidaje da hanyoyi da dai sauransu.

Amma a shekarun baya-bayan nan, da dama na cewa, ana amfani da ita a matsayin makami a hannun Indiyawa mabiya addinin Hindu a gwamnatin jam'iyyar BJP wajen ruguza gidaje da rayuwar al'ummar Musulmai tsiraru.

Kuma galibin wannan rusau ana aikata su ne a jihar Uttar Pradesh da ake fama damatsanancin matsalolin siyasa.

Na baya-bayan nan da ya auku shi ne a ranar Lahadi, lokacin da mahukunta a birnin Prayagraj da a baya ake kira Allahabad, suka rusa gidan wani fitaccen dan siyasa, Javid Mohammad, da suke zargin cewa ginin da ya yi haramtacce ne - zargin da iyalansa suka musanta.

Masu suka na cewa rusa gidan mutumin da aka alakanta da saɓa dokokin shari'a kamar yada ake zargi, kawai dai ana masa wannan hukunci ne kasancewar ya yi fice wajen caccakar gwamnati.

Kwana guda bayan rusa ginin nasa, 'yan sanda sun cafke shi, suna zarginsa da kitsa kazamar zanga-zanga a birnin, tsakanin Musulmai kan ɓatanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad, da Nupur Sharma, tsohuwar kakakin BJP ta aikata.

Ms Sharma da fari an dakatar da ita daga jam'iyyar, sai dai masu zanga-zanga na son ganin an cafke ta.

Shugabannin BJP sun kare matakinsu, suna mai cewa "bai saɓawa dokokin shari'a ba".

Sai dai rusau din - wanda ya ja hankali da alakanta yanayin da yadda Isra'ila ke amfani da manyan makamai a yankunan Falasdinawa - ya fuskanci kakkausar suka a Indiya da mamaye kanun labarai a jaridun duniya, masu suka na cewa aikata irin haka ya saɓawa doka.

A wani mataki da ba a saba gani ba, tsofaffin alkalai na da da na yanzu sun aike da wasika zuwa ga babban alkalin alkalai suna mai cewa amfani da buldoza "bai dace da dokoki ba" suna umartar kotu ta dau matakin gaggawa kan "cin zarafin da ake yi wa Musulmai a Indiya".

Yogi Adityanath's supporters with toy bulldozers

A wani kanun labarai masu zafi da jaridar India Express ta wallafa, tsohon Minista Kapil Sibal ya rubata cewa "buldoza ba ta da alaka da haramtaccen gini, yana da alaka ne da wane ne mutum kuma mene ne matsayinsa".

"Yana da alaka da abin da muke faɗawa al'umma. Yana da alaka da addini, al'umma da mutum karan kansa, da abin da yake bautawa.

"Yana da alaka da muryarta. Lokacin da ana rusa mun gidana da buldoza, ba rusa mun gidana kawai ya yi ba, ya kuma danne 'yancina na tofa albarkacin baki."

Amfani da buldoza ya fuskanci kalubale har a gaban kotun koli, kuma babbar kotun na cewa "an yi hakan ne bisa tsarin doka kuma bai kamata a mayar da martani ba".

A farkon wannan shekarar, na ci karo da wasu mutane da ke cikin fushi, lokacin da nake kawo rahoto kan zaben Uttar Pradesh, lokacin Ministan Yogi Adityanath ke neman a sake zabensa. (Ya lashe zaɓen kuma yanzu yana mulki a sabon wa'adi na biyu).

A wani gangami da aka yi kan tittuna, tawagar wasu magoya-baya sun taho wajen da kananan buldoza na wasan yara launin ruwan ɗorawa.

Suna ta ɗaga buldozar ta roba, suna ta rawa da kaɗe-kaɗe a kafar talabijin, suna ambatar "woh bulldozerwala baba phir se aayega (uban buldoza ya dawo)".

"Uban Buldoza" suna ne da aka bai wa Mista Adityanath da wasu kafofin labarai suka yi, sai dai an soke amfani da sunan lokacin da abokin hamayyarsa Akhilesh Yadav ya yi amfani da kalmar a gangamin zabe.

Mista Yadav ya yi amfani da sunan a fakaice, amma babban dan jarida Sharat Pradhan ya ce "BJP suna amfani da wannan domin cin ribarsu saboda shi ne inkiyarsa".

A birane da dama, a cewarsa, an ajiye buldoza a gangamin yakin neman Mista Adityanath bayan ya lashe zabe, an gabatar da motar har a gaban ginin majalisa lokacin bikin nasararsa.

A protest in Delhi against demolitions

Asalin hoton, Getty Images

Babban ɗan jarida Alok Joshi ya ce Mista Aditynath da fari ya umarci a yi amfani da buldoza shekaru biyu da suka gabata kan wani kasurgumin mai akata laifi, Vikas Dubey, wanda ake zargi da kashe 'yan sanda takwas, da far wa dan siyasa, Mukhtar Ansari.

Hotunan bidiyon rusau da aka yi wa kadarorinsa an haska a tashar talibijin din kasar, abin da ya kai ga wasu 'yan kasar na yabon gwamnati kan matsayar da ta dauka kan masu aikata laifi.

"Sai dai yanzu ya kasance wani salo da ake amfani da shi wajen nuna tsangwama kan masu adawa da sukar gwamnati, musamman Musulmai," a cewar Mista Joshi.

Amfani da buldoza ya kasance abin da duniya ke nuna kokawa a kai, amma Mista Joshi, ya ce ya kasance abin da ya sauya sauya siyasar Mista Adityanath da kuma samun goyon-baya wajen Firaminista Narendra Modi.

A lokacin wata ziyara da ya kai cikin watan Disamba, Mista Modi ya ce, "Lokacin da buldoza ke bi ta kan mafiyoyi...tana rusa ginin da ake cewa ya haramta, amma mutane da ake yi wa hakan na cikin zafi sosai."

Bayan wasu kalamai da Firaministan ya yi, ana amfani da buldoza a kokarin ingiza rikicin addini a farkon shekarar nan a jihar Madhya Pradesh da birnin, Delhi, wanda kai-tsaye ya ke shafar Musulmai ta hanyar lalata musu gidaje da shaguna da wajen sana'o'i.

"Babu wata kotu da ta umarci rusa gidajen mutane, ko da kuwa sun aikata laifuka ko kuma an yanke musu hukunci.

"Don haka lokacin da mahukunta suka aika buldoza, hakan na kunshe da sakon siyasa kai tsaye - duk wanda ya yi adawa kan amfani da buldoza shi ma za a aike masa buldoza," a cewar Mista Joshi.

Presentational grey line
Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda aka rushe gidajen Musulmai bayan zanga-zangar adawa da ɓatanci ga Annabi
Presentational grey line