Yadda 'yan Afghanistan suke rayuwa cikin kunci a otal-otal da ke Birtaniya

    • Marubuci, Daga Alice Cuddy, Ali Hamedani, Anna Adams and NJ Convery
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, UK Insight
  • An wallafa

Yayin da Birtaniya ke karbar 'yan gudun hijirar da yakin Ukraine ya raba da muhallansu, ana ci gaba da sanya ayar tambaya kan ko an yi abin da ya dace ga 'yan gudun hijirar Afghanistan da suka nemi mafaka a kasar sama da watanni bakwai da suka gabata.

A lokacin da mayakan Taliban suka karbe ikon Afghanistan a bara, tsoro da fargaba sun mamaye zukatan 'yan kasar kan makomar rayuwarsu, don haka suka fara tserewa wasu kasashen. Birtaniya na daga cikin kasashen da suka kwashe mutane da dama, inda ta taimaka wa mutane sama da 15,000.

Sai dai watanni bakwai bayan nan, yawancin mutanen na rayuwa ne a otal-otal da ke kasar ba tare da sanin lokacin karewar hakan ba. Ofishin harkokin cikin gida na Birtaniya ya yi kiyasin cewa ana kashe sama da fam miliyan daya ga mutanen a kowacce rana.

Yawancin 'yan gudun hijirar Afghanistan din wadanda a baya sun yi aikin gwamman shekaru da gwamnatin Birtaniya, sun shaida wa BBC irin fadi-tashin da suke yi na kula da iyalansu a dakunan otal, da kuma fatan inganta rayuwarsu nan gaba.

"Iyalaina suna bukatar gidan kansu domin gina sabuwar ingantacciyar rayuwa," in ji wata mace.

'Ba na so na takura wa kowa'

Mun kai ziyara wani otal din da a yanzu ya zama sansanin 'yan gudun hijirar gwamman 'yan Afghanistan. A gefen dakin karbar baki, maza ne suka taru suna tattaunawa kan sabbin labaran da suke ji daga kasarsu, labaran da suka shafi iyalai, 'yan uwa da abokan arzikin da suka baro a gida, da rayuwarsu a Birtaniya.

Daga wani dan wuri kana jiyo muryoyin da ke nuna iyalai na zaune a wannan wuri.

Rayuwa tare da matarshi da 'ya'ya shida abu ne mai matukar wuya ga Farid Rahmani, wanda ya kwashe shekaru da dama yana aiki a ofishin jakadancin Birtaniya a matsayin tafinta. Sun ba shi katon gida wadatacce a wajen birnin Kabul.

A lokacin da Taliban suka karbe iko da kasar a watan Agustan bara, ya ji tsoron kada shi da iyalansa su shiga mawuyacin hali saboda aikin da ya yi da ofishin jakadancin Birtaniya, ya damu kan makomar matarsa da 'ya'yansa idan suka zauna a kasar karkashin ikon Taliban.

A lokacin da aka kira shi ta wayar tarho, da shaida masa cewa za a ba shi dama shi da iyalansa su fice daga kasar zuwa Birtaniya, kuma minti 15 kadai aka ba shi ya isa filin jirgin sama, inda cincirindon 'yan Afghanistan ya mamaye.

A baya, Farid na aikin kwanaki shida a mako, yana kuma jin dadin zama cikin 'ya'yansa a ranar da ba ya aiki. Amma a yanzu ba shi da motar hawa, da takaitattun hanyoyin sufuri, da kyar yake barin dakin otal din da suke zaune, kullum yana kai 'yarsa makarantar Nazire ya kuma dawo da ita. An rarraba iyalanshi zuwa dakuna hudu na otal, yana kuma amfani da daki guda tare da matarshi da 'ya'yanshi mata biyu.

"Babu abin da muke yi a nan. Wannan ne dalilin da ya sa nake zama cikin kunci, ba mu taba zaton za mu zauna a otal sama da makonni hudu ba. Shafe lokaci mai tsawo a otal babu dadi, akwai takura gaskiya."

Iyalansa sun iso Birtaniya da tsirarun sutura, baya ga wadda ke jikinsu, duk da haka Farid ya nuna godiya kan tallafin da ya samu. Baya ga wurin zama, ana bai wa iyalan abinci, amma su ke yin wankin kayansu. An sanya yaran a wata makaranta, sannan gwamnatin Birtaniya na ba su wasu 'yan kudade domin kula da rayuwarsu.

Kamar sauran iyalai da muka zanta da su, shi ma Farid ya na da na shi mafarkin na samun aiki da gina ingantacciyar rayuwa da iyalansa. Ya ce 'ya'yanshi na yawan tambayar ko yaushe za su koma nasu gidan, inda za su samu filin wasa da cin abincin da ransu ke muradi. Amma ba shi da amsar ba su, sai dai ya yi shiru.

"Ba ni da abin cewa, ban san tsawon lokacin da za mu kwashe a otal ba, watakila wata guda, ko biyu ko ma uku. Jami'in ofishin cikin gida ya ce samun gida a Birtaniya abu ne mai matukar wuya," in ji Farid.

Yana da damar aiki a Birtaniya, amma rashin sanin inda zai zauna, yana janyo koma-baya ga samun aikin nasa. "Idan za su ba ni gida a ko ina a kasar nan, ba zan ki amincewa ba, zan iya yin kowanne aiki. Zan iya aiki a kanti ko ma ina ne ba ni da matsala. Ba na son takurawa kowa, ciki har da gwamnati."

' Muna son sake gina rayuwarmu'

Farid daya ne daga cikin 'yan gudun hijirar Afghanistan 12,000 da ke rayuwa a otal. Can a wani bangare na kasar, mun sake ganin wasu iyalan da suka rike manyan mukamai a gwamnatin kasar da Taliban ta rusa. A yanzu tana zaune a daki daya a wani otal tare da mijinta da 'ya'yanta.

"Muna godiya ga gwamnatin Birtaniya da ta kubutar da rayuwarmu. Abu ne mai muhimmanci da muka zo nan, babbar dama ce da yawancin 'yan Afghanistan ba su samu ba.

"Sai dai mun gaji da zaman otal, abin babu dadi. Idan da hali muna son a ba mu muhallanmu domin sake gina rayuwarmu," in ji ta.

Shi ma wani magidanci da ya yi aiki tare da sojin Birtaniya, da a yanzu yake rayuwa shi kadai a dakin otal bayan an raba shi da matarsa mai juna-biyu da 'ya'yansu a lokacin da suke gudun ceton rai, ya shaida wa BBC cewa kullum yana mafarkin sun sake haduwa da iyalansa, da komawa aikin da yake yi na shago.

A yanzu rayuwar shi baki daya a cikin daki ta ke. Yana shafe tsawon rana ta wayar tarko da 'yan uwansa da ke Afghanistan, sai hira da sauran 'yan kasar da ke otal din da yake, yana kuma kokarin koyon harshen Turanci ta hanyar amfani da shafukan Youtube.

A wani sako da ke dakinsa, akwatun kayansa ne, sai farantan abincin da ba a ko bude ba akan wani teburi, ya ce ba ya iya cin abinci saboda tunanin 'yan uwa da iyalansa da ke Afghanistan.

"Abin da na ke son gwamnatin Birtaniya ta taimaka min shi ne a dauko iyalina. Ina son manta duk abin da ya faru baya, na fara sabuwar rayuwa ," ya fada cikin hawaye. "Idan ina tare da iyalina, ina ganin 'ya'yana da na ke so wasu daga ciki su zama likitoci wasu kuma injiniya."

Ofishin cikin gida a Birtaniya, ya ce zamansu a otal na takaitaccen lokaci ne, za su yi aiki kafada-da-kafada da hukumomi domin sama musu matsuguni na dindindin.

A wata sanarwa da ofishin ya aike wa BBC, ya ce suna alfahari da suka bai wa sama da iyalai 4,000 muhalli, za kuma su ci gaba da tuntubar hukumomi domin samawa iyalan Afghanistan matsuguni, domin sake sabuwar rayuwa.

Sai dai sun yi kira ga gwamnati ta shiga lamarin domin taimakawa.

A wata wasika ta baya-bayan nan, 'yan majalisu da kungiyoyin bada agaji sun yi kiran a samar da abin da suka kira shirin "Gidajen 'yan Afghanistan" kamar yadda aka bai wa wadanda suka tsere daga Ukraine tallafi, domin sama musu mafita, ciki har da sanya kungiyoyin da ke aiki a matsayin masu daukar nauyin 'yan gudun hijirar.

'Yan gudun hijirar Afghnistan na bin Birtaniya bashin mutuntawa, sannan ba zai yiwu su iya gina musu sabuwar rayuwa a otal ba, in ji wasikar.

Dan majalisa daga jam'iyyar Conservative, Damian Green, wanda ya rattaba hannu kan wasikar, ya bayyana ajiye 'yan gudun hijirar a otal din mazabarsa da abun a yaba.

"Wasu daga ciki an ba su aikin yi, amma ba za su fara ba saboda ba su da takamaimai wurin zama," kamar yadda ya shaida wa shirin BBC.

Kungiyoyin agaji sun nuna damuwa kan makomar 'yan gudun hijirar Afghanistan da ke zaune a otal.

"Abu ne da sam ba za a amince da shi ba, sun shafe watanni a Birtaniya, amma dubbansu suna rabe a kananan dakunan otal, a cunkushe, babu wadatar wuri,'' in ji Yasmine Ahmed, daraktar kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch a Birtaniya.

"Yawancinsu sun fuskanci tashin hankalin da ba su taba tsammani a rayuwarsu ba, su na kuma fama da matsananciyar damuwa. Ba su san takamaimai lokacin da za su samu muhallansu domin kauce wa zaman takurawa wasu."

Ga Farid, ba zai samu gidan kan shi cikin takaitaccen lokaci ba."Zaman otal babu dadi, akwai takura. Amma na tabbata idan muka samu matsuguni, za mu samu damar mai yawa a nan Birtaniya da za mu gina sabuwar rayuwa."