Afghanistan: An sake hada jaririn da ya bata a rikicin Kabul da iyayensa

An wallafa

Jaririn da ya ɓata yayin hayaniyar Kabul, lokacin da Amurka ke kwashe 'yan Afghanistan a karshe dai ya sake haduwa da iyayensa.

Taliban ta kwace iko da kasar a watan Agustan 2021, kuma 'yan Afghanistan da yawa sun yi ta kokarin ficewa daga kasar ido rufe.

An mika wa wani sojan Amurka Sohail Ahmadi dan wata biyu da haihuwa ta kan wayar da aka yi katanga da ita, domin ya kare shi daga turmutsutsun da ake yi na kokarin shiga filin jirgin Kabul.

Iyayensa na cikin wadanda aka yi wannan turmutsutsun, amma yanzu an gano Suhail.

Bayan tashin hankalin da aka shiga da kuma wani dan kwarya-kwaryar neman yaron da aka yi, mahaifinsa Mirza Ali Ahmadi da yake aikin tsaro a ofishin jakadancin Amurka da mahaifiyar jaririn Suraya da wasu 'yan uwan jaririn hudu an kwashe su an kai su Amurka.

Watanni masu yawa aka share babu ɗuriyar dan jaririn nasu.

Amma bayan karanta wani labarin kamfanin dillancin labarai na Reuters kan iyalan da ke neman Sohail, a watan Nuwamba, sai ya nemi gidan direban tasin mai suna Hamid Safi.

Mista Safi ya ce ya tsinci Sohali a kasa shi kadai yana kuka a filin jirgin sama, in ji kamfanin dillancin labaran.

Bayan kokarin neman iyayen jaririn, ya yanke shawarar ya dauki yaron ya kai gida wajen matarsa ta hada shi da iyayensa, domin su girma da yaransa.

Sun sanya wa yaron suna Mohammad Abed kuma sun rika wallafa hotonsu a Facebook din Safi tare da jaririn.

Yayin da aka tabbatar da cewa shi ne jaririn da ake nema, kakan yaron Mohammad Qasem Razawi, wanda yake zaune a arewa maso gabashin yankin Badakhshan, ya yi tafiya mai nisa zuwa Kabul domin karbar jikansa.

Haka kuma, Mista Safi ya ki bayar da jaririn kuma ya nemi shi ma a dauke shi da iyalansa a kai su Amurka, in ji Reuters.

Bayan kwashe kusan mako bakwai ana yarjejeniya - bayan wata tsarewa da aka yi wa Mr Safi na dan lokaci - 'yan sandan Taliban sun shirya haduwa tsakanin iyalan biyu a ranar Asabar aka dawo da jaririn, in ji Reuters.

Iyayansa sun ce sun ji matukar dadi bayan haduwa da yaron nasu ta hoton bidiyo.

"An yi raye-raye an wakoki da murna mai yawa, tamkar aure aka sake yi," in ji Mr Razawi.

Suna fatan haduwa da dansu a kusa a Michigan inda suke zaune yanzu.