Matsalar tsadar rayuwa: Yadda tashin farashin kayayyaki ya haifar da zanga-zanga da 'yan gudun hijira

Matsin tattalin arziki a Sri Lanka ya haifar da zanga-zanga

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Matsin tattalin arziki a Sri Lanka ya haifar da zanga-zanga
    • Marubuci, Daga Swaminathan Natarajan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

Fusata kan tashin gwauron zabin kayayyaki ta kara ta'azzara zuwa gagarumin rikicin siyasa a kasar Sri Lanka.

Wannan kasa ta tsibiri na da kudi kalilan na shigar da kayan abinci da makamashi da karancin abubuwan amfani ya haddasa zanga-zangar kan titina da ke yin barazanar hambarar da gwamnati.

Labari irin wannan na faruwa a kasar Peru mai nisan dubban kilomita, inda shugaba Pedro Castillo ya kafa dokar hana zirga-zirga a Lima babban birnin kasar a makon jiya, bayan wata zanga-zangar gama-gari kan tashin farashin mai da taki.

Amma wadannan sun zarta na kasa daya kacal da yanzu haka ke fuskantar matsin tattaalin arziki, yayin da yakin kasar Ukraine ya sa farashin danyen mai kara hauhawa zuwa dala 100 kan ko wace ganga.

Farashin kayan abinci na duniya sun kara hauhawa tun bayan da aka fara tattara bayanai shekaru 60 da suka gabata kamar yadda alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka nuna, wanda ya tashi zuwa kashi 13 bisa dari a cikin watan Maris, bayan karuwa mafi girma da ya yi a cikin watan Fabrairu.

BBC ta tattauna da mutane daga kasashe shida don gano yadda suke fama da tsadar rayuwa.

Sri Lanka: 'Mun kasa samun ko da abubuwan bukatunmu na yau da kullum'

Tsananin hauhawar farashi da karancin abubuwan amfanin yau da kullum na kara ingiza mutane zuwa daukar tsauraran matakai a kasar Sri Lanka.

Lokacin yakin basasar kasar, dubban 'yan kasar ta Sri Lankan sun zabi yin bulaguron cikin teku mai cike da hadari don neman mafaka a kasar Indiya.

Yanzu matsin tattalin arziki ne ke sa mutane barin kasar.
Bayanan hoto, Yanzu matsin tattalin arziki ne ke sa mutane barin kasar.

Mary Clara na daga cikin sahun farko na 'yan gudun hijirar kasar Sri Lanka 16 da suka zo Tamil Nadu a cikin mako na uku na cikin watan Mayu.

Ta tsallake tsukin hanyar cikin teku a wani karamin kwale-kwalen kamun kifi ita da jiririnta mai watanni hudu da kuma mijinta.

"Farashin kusan komai ya tashi sama. Yana da matukar wahala ka sayi abubuwan amfani kamar sun madarar gari wa jaririna,'' Clara ta bayyana.

Alkaluman hukuma sun nuna hauhawar farashin kayan a Sri Lanka zuwa kashi 15 da digo daya bisa dari a cikin watan Fabrairu - mafi girma a cikin shekaru goma - kana hauhawar farashin kaya abinci ya zarta zuwa kashi 25 da digo bakwai bisa dari.

Farashin shinkafa- abincin da aka fi amfani da shi- ya tashi sama zuwa sama da dala daya kan ko wane kilo. Farashin man fetur ya linka fiye da sau biyu.

"Mijina aikin fenti yake yi amma yanzu ya shafe kwanaki bai samu aikin ba. Tun bayan tashin farashin kayayyakin amfanin yau da kullum, mun kasa samun sayen abubuwan da muka fi bukata,'' Clara ta bayyana.

Akasarin sassan kasar na fuskantar yawan daukewar wutar lantarki a ko wace rana har na tsawon sa'oi 10 zuwa 12. Gwamnati na kashe fitilun bakin hanyoyi don tattalin wutar lantarkin.

Matsanancin daukewar wutar lantarki na nufin cewa turakun wayoyin salula ba za su iya aiki ba, kana wasu asibitocin dole suka rika soke yin aikin tiyata.

Rahotannin kafafen yada labaran kasar sun ce mutane akalla biyar ne suka mutuwa sa saboda galabaita a yayin jiran dogon layin sayen man fetur da kuma man disal a cikin makon na biyu na watan Maris.

Ma'aikata kamar su mijin Clara na samun dala biyar a ko wace rana amma iyalan mutum biyar na bukatar dala takwas wajen girka cikakken abinci.

Clara na gab da fadawa cikin matsalar yunwa na tsawon kwanaki da danna kafin zuwanta kasar Indiya kana halin da ake ciki na kara muni a kasar Sri Lanka.

Tana sa ran wasu da dama za su biyo bayanta muddin al'amura ba su daidaita ba.

Lebanon: 'Za ka ga mutane na neman abinci a cikin bola'

"Za ka ga mutane na neman abinci a cikin bola. Abin bakin ciki ne,'' in ji Mariel Aoun.

Mariel Aoun a gidanta

Asalin hoton, Mariel Aoun

Bayanan hoto, Hauhawan farashi ya hausa sama da kashi 200 a cewar Mariel Aoun a Lebanon

Shekarunta 64 kuma tana zaune a birnin Beirut, wanda ya danganta irin kudin da ta samu daga hayar gidaje biyu.

Kasar Lebanon, wacce rikicin siyasa da matsin tattalin arziki da ake ciki suka dabibaye tun ma kafin na baya-bayan nan, na da alkaluma na hauhawar farashin kayayyaki mafi girma a duniya - sabbin alkaluma na watan Fabrairu kashi 215 bisa dari ne na alkaluman kididdigar shekara-shekara.

"Bayan fara yaki [a kasar Ukraine] al'amuran sun kara muni. Kayan abinci sun yi batan dabo a shagunan kayan masarufi, kana idan an sake samu bayan makonni biyu, farashinsu kan linka,'' in ji Aoun.

Matsin tattalin arzikin kasar ya kara ta'azzara sakamakon annobar korona da kuma babbar fashewar sinadarin iskar ammonium nitrate da ta mamaye tare da lalata tashar jiragen ruwa ta birnin Beirut a watan Agustar shekarar 2020.

"Saboda fashewar, gidana ya lalace. Na so in yi amfani da kudin da na tara wajen yin gyare-gyare, amma banki ya ki dawo min da kudina.''

Amma su kan su bankuma na fuskantar karancin kudi.

"Yanzu ba za ka iya biyan kudin komai ba ta hanyar amfani da katin biyan kudi. Dole sai ka biya kashi 50 bisa dari a tsabar kudin.''

Aoun ta ajiye wasu kayyakin abincin da hatsi a gidanta. Ta kuma zaftare yawan yadda ta ke saye-sayen kayan abincin.

Yaki ya kara tasiri ga tsadar kayan abinci a Lebanon

Asalin hoton, Mariel Aoun

Bayanan hoto, Yaki ya kara tasiri ga tsadar kayan abinci a Lebanon

"Yanzu ba na sayen cukwui - na kan yi a gidana. Ba na iya sayen avocados, wanda nake matukar so.''

Matsanancin daukewar wutar lantarki sun sauya rayuwarta. Tana biyan dala 125 wajen amfani da injin janareta na tsawon sa'oi goma a rana, amma wutar lantarkin ba ta wadata ba.

"Ba zan iya amfani na firji da na'urar wankin kaya a lokaci daya ba. Dole in kashe na'urar dumama gidana idan ina bukatar yin girki. Yak an dauki tsawon lokaci kafin ka kammala ayyukan yau da kullum.''

"Kusan duka kayayyaki farashinsu ya tashi sama zuwa linki goma a cikin shekaru biyu da suka gabata. Lita ashirin na man fetur a baya fan 20,000 ne na Lebanon - yanzu rabin miliyan!" ta kara bayyanawa.

Aoun ta ce ko wace rana na zuwa da karin sabbin munanan labarai kuma ba ta ganin abubuwa za su yi sauki nan kusa.

Turkiyya: 'Muddin abubuwa suka cigaba da tafiya a haka, bani da wani wurin da zan koma'

Ibrahim ya tsere daga kasar Syria zuwa Istanbul a shekarar 2016. Kamar sauran 'yan gudun hijira har yanzu bai samu matsayin takardar zama ɗan kasa ba, amma ya samu wani aikin yi.

Ibrahim
Bayanan hoto, Ibrahim ya nemi masauki mai sauki

Hauhawar farashin kaya a kasar Turkiyya ya kai girman na shekaru 20 a kan kashi 54 da digo 44 bisa dari. Hakan ya haifar da koma bayan wajen yanayin kashe kudaden masu karamin karfi kamar Ibrahim.

A shekarar da ta gabata ba shi da aikin yi har na tsawon watanni biyu. Dan uwansa da ke aiki a Dubai ya tallafa masa da kudi.

Ya tashi daga gida mai daki biyu da yake haya tare da wani abokinsa ya koma wani wuri daban.

"Yanzu muna gida daya tare da ma'aikata da dama. Ina da karamin daki ama dole mu rika amfani da wurin dafa abinci da ban-daki daya da sauran ma'aikata.''

Shi ma Ibrahim na kokarin rage yawan kudaden da yake kashewa.

"Na kan fita sau daya zuwa uku a wata zuwa wurin cin abinci da abokaina. Bana ma taba tunanin zuwa wurare masu tsada.''

Zuwan baki 'yan yawon bude ido na karuwa, amma kuma Ibrahim gudanar da ayyuka kamar su samar musu da motocin tasi na haya, da shirya zuwa wuraren bude ido da kuma taimaka musu da zuwa wuraren sayayya don samun karin kudin shiga.

"Buri na shi ne in koma wuri mai daki daya amma ban san iya tsawon lokacin da zan shafe ina jira ba. Duba da yadda al'amura ke tafiya, abubuwa sun wuce karfina. Shi kan sa kudin hayar da nake biya kusan yawan abinda nake samu ne - wanda ba ya rage min komai na wanda dan biya wasu kudaden.''

Bayan da tuni ya zama dan gudun hijira, Ibrahim ya bayyana cewa muddin abubuwa suka cigaba da muni, ba shi da wani wurin da zai koma.

Najeriya: 'Kana bukatar yin aiki biyu tukuru kafin ka samu yanayin rayuwar da kake so'

"Komai ya kasance babu wani ci gaba. Matsalolinmu na faruwa ne saboda rashin kulawa,'' in ji Aisha Falke.

Aisha Falke

Asalin hoton, Aisha Falke

Bayanan hoto, Aisha Falke ta dora laifin ga rashin shugabanci ga matsalar ƙasarta

Mai kananan 'yaya biyu, tana zaune a Abuja, Marubuciya a shafin intanet da kuma mai zayyanawa da dinka tufafin zamani ce.

"Muna da kawo shawarwari game da harkar kasuwanci don samu karin kudin shiga. Akwai gajiyarwa. Yana nunawa a jikina - kalli furfura ta.''

"Nan gaba za ka bukaci ka yi aiki biyu tukuru kafin samu yanayin rayuwar da kake bukata.''

Najeriya ita ce mafi girma a Afirka wajen samar man fetur, amma ta gaza wajen tace danyen mai a cikin gida kuma ta dogara ga shigowa da kaya.

Tsananin tsadar man a kasuwar duniya ya riga ya haifar da karancin albarkatun man fetur a kasar, tare da ta'azzara hauhawar farashin sauran kayayyakin amfanin yau da kullum da ayyuka.

Falke ta bayyana cewa kudaden da ta ke kashewa a ko wane wata tafiyar da harkokin cikin gidanta ya kara sama da kusan rabi a cikin shekara.

"Komai ya yi tsada - shinkafa, da burodi, da kayan marmari, da sufuri, da naman miya, da man girki… Mun saba cin naman kaji a kullum, amma yanzu farashin kaji ya kusa linkawa.''

Karancin wutar lantarki da na man fetur na kara mummunan tasiri kan kasuwancinta.

"Kostomomina na amfani da kudadensu wajen sayen kayan abinci da magunguna fiye da dinka sabbin tufafi. Tufafi wani abu ne na garari a yanzu."

Tanzania: 'Albashina na wata daya yawanci kan kare bayan kwana 20'

Su kansu wadanda ke zaune a nesa da manyan biranen kasuwanci da tattalin arziki ba su tsira daga wannan halin matsi ba.

Anny Laizer ta ce a al'ummar Massai na cikin wani hali saboda tsadar kayayyaki

Asalin hoton, Anny Laizer

Bayanan hoto, Anny Laizer ta ce a al'ummar Massai na cikin wani hali saboda tsadar kayayyaki

'Yan kabilar Massai na bin al'adar yanayin rayuwar makiyaya wanda galibi ke da wadatuwa, da dogaro da shanu a matsayin arzikinsu. Amma su kan su matsin tattalin arzikin duniya ya shafe su.

"Abincin gargajiyarmu ya kunshi madarar shanu da nama,'' in ji Anny Laizer.

Yanzu Laizer na zaune a birnin Arusha kuma tana aiki da wata kungiya mai zaman kan ta, amma tana tuntubar mutanenta da har yanzu suna bin tsarin yanayin rayuwar zamanin da.

"A shekarar bara za ka iay safen kilogiram 5 na albasa a kan dala 2, amma yanz waken dala 5 ne. Man girki farashin say a tashi sama zuwa kashi 50 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. Farashin wutar lantarki shi ma ya karu. Ba kowa yake da hali ba,'' in ji Laizer.

Bushewar kasar noma da kiwo ya riga ya tilasta wa iyala rage yawan garken shanunsu, kuma The Lazier ta bayyana cewa wasu mazan a kauyenta sun kaura zuwa garuruwa don neman aiki kamar irin su gadi.

Wani dan kabilar Massai

Asalin hoton, Anny Laizer

Bayanan hoto, Anny Laizer ta ce a al'ummar Massai na cikin wani hali saboda tsadar kayayyaki

Laizer na tallafa wa iyayenta da kannenta mata, amma sauran danginta ma kan nemi taimako daga gare ta su ma.

"Albashina dala 250 a ko wane wata. Galibi yak an kare bayan kwanaki 20. Fadi-tashi ne matuka - na kan rika samun wayoyi da dama a ranar da na karbi albashi ana neman taimako na.''

Korea ta Kudu: 'Ba zan ci bashin kudi ba saboda hakan zai jefa ni cikin kangin basussuka'

'Yan kasar Korea ta Kudu na fuskantar na su adadin hauhawar farashin kayan mafi girma a cikin shekaru takwas. Manyan labaran kasar kan tsadar kayayyaki ka iya kasancewa kashi 3 da digo 7 bisa dari ne, amma farashin wasu kayayyakin abincin ya kara hauhawa fiye da hakan, da ya tilasat wa da dama kamar su Lee So-jung sauya yanayin tafiyar da rayuwarsu.

Wani lokaci Lee So-jung ta ce tana cin kwalama maimakon abinci don rage kashe kudi

Asalin hoton, Lee So-jung

Bayanan hoto, Wani lokaci Lee So-jung ta ce tana cin kwalama maimakon abinci don rage kashe kudi

"Ni daliba ce. Na kan samu kudin kashewa daga iyayena, kuma na kan samu 'yan kudi ta hanyar yin aikin wucin-gadi. Saboda tsadar rayuwa kudina na karewa cikin sauri. A wasu lokuta na kan koma cin kayan kwadayi ko shan gahwa a maimakon cin abinci sosai na rana,'' in ji Lee So-jung.

Ta rage yawan tafiye-tafiye zuwa gidajen cin abinci, kuma ko da ta je din ma ta kan zabi cin taliya a maimakon sushi.

Korea Kudu ta dogara kacokan ne kan man da ta ke shigar da shi wajen bunkasa tattalin arzikinta - a shekarar bara kasar ta shigar da man da ya kai dala 67. Hauhawar farashin kayan wanda yakin kasar Ukraine ya kara haddasawa ya yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin.

"Tsadar rayuwa a kasata karuwa yake. Hakan na nufin 'yan zamani irina ba za mu iya samun mallakar gidajen kashin mu da muke so ba, da cin irin abincin da muke so ko sayen irin tufafin da muke so.''

Iyalan Lee So-jung da wasu kawayenta na samun tallafi daga gwamnati, amma tana daukar irin na ta matakan.

"Ba zan rika karbar bashin kudi ba saboda hakan zai saka ni cikin kangin basussuka. Ina rage yawan kudaden da nake kashewa a maimakon haka.''