Mutumin da ke farautar 'yan Najeriya da ke iya rikiɗewa zuwa mage

- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC
- An wallafa
Ɗauke da wuka mai kaifi, lasifika kuma sanye da baƙaƙen tufafi, Gbenga Adewoyin na kama da irin mafarautan zamanin da ya shude, mai sayar da maganin gargajiya ko masu sanƙira yayin da ya ke karaɗe kasuwanni a kudu maso yammacin birnin Ibadan da ke Najeriya.
Gargaɗi: Wannan maƙala na ɗauke da bayanan da ke iya tada hankali ko ɓacin rai ga mai karatu
Mutane na tarwatsewa wasu kuma na fitowa kallo idan ya soma sanar da sakonsa. "Duk mutumin da zai iya kawo shaidar wani salon tsafi ko sidabaru ko tsibbu, zan ba shi naira miliyan biyu da rabi," yana tafe yana bada sanarwar a harshen Yarbanci da Turancin Ingilishi.
Matashin mai shekara 24 da bai yarda da cewa akwai wani ubangiji ba, ya kasance wani ɗan tawaye da ke fitowa yana nuna adawarsa da duk wani salon asiri ko tsubu a tsakanin addinan ƙasarsa.
Imani da wasu al'adu da tsafi ko sihiri abu ne da ya zaman ruwan dare a Najeriya, akwai wadanda ke alakantasu da addinai ko na Kirista ko Musulunci, a cewar wani rahoto da cibiyar Pew ta fitar a 2010.
'Yan Najeriya da dama na da yaƙinin cewa sihiri ko tsubu na iya sauya mutane su koma sifar mage, ba su kariya daga yankar wuka ko kuma su ga bayyanar kudi a cikin tukunyar kasa.
Wannan ba wai marasa ilimi kaɗai ba ne ke da irin wannan yarda, mutane da dama har a kololuwar matakin ilimi na da yarda kan irin waɗannan abubuwa.
Dakta Olaleye Kayode, wani babba malami ne a fanin ilimin al'adun Afirka a jami'ar Ibadan, ya shaida wa BBC cewa tsafin da mutane ke yi don kuɗi - inda ake cire sassan jiki a yi sihirin kudi a cikin tunkunya - na aiki sosai.
Kuɗaɗen nairar da ake samu a tsafin "aljannu ke kwaso su daga cikin bankuna," a cewarsa.
Jude Akanbi, malami a wata makarantar falsafar addini da ke Abeokuta, shi ma yana da yarda sosai a kan sihiri.
"Iya komawa sifar mage, mutum ya ɓace ya dawo, duk abubuwa ne mai yiwuwa tsakanin al'adu da addinan mutanen Afirka.
"Duk da cewa wani na iya jinsa banbarakwai, kamar tasuniya, daga abubuwan da muke gani da ji, duk wannan mai yiwuwa ne," a cewarsa.
Irin wadannan tunani, musamman batun wai ana iya amfani da sassan jikin mutum da magani a yi tsafi a tukunyar kasa, ya haddasa karuwar kashe-kashe don tsafi a kasar, inda akasari aka fi hallaka mata marasa aure.
"Ina takaicin ganin matasa na shiga wannan harka na kashe mutane don tsafi.
"Idan kuɗin tsafi na aiki, da mun ga tasirinsa a tattalin arziki shekaru aru-aru, tun lokacin da mutane ke da wannan yarda," a cewar Mista Adewoyin.
Yana Ibadan, na jihar Oyo a rana ta biyu da jeren tafiya kashi 3 da ya tsara yana mika tayin naira miliyan biyu da rabi, kudaden da aka tara har a shafin Tuwita, kuma za a bai wa duk mutumin da ya fita ya nuna karfinsa na tsafi.
"Wannan wukar na mutanen ne da suke bugun ƙirjin cewa wuka ba za ta yanke su ba," a cewarsa.

Asalin hoton, Getty Images
Diga ayar tambaya ko kalubalantar tsafe-tsafe abin alla-wadai ne a tsakanin al'umomin Najeriya da dama.
Ka fitowa fili kana bayyana ra'ayi kan irin wannan tunani, kamar yadda Mista Adewoyin ke yi a kasuwa, na da haɗari. Ana iya kama shi kan laifin ɓatanci ko fusatatun matasa su hallaka shi.
"Babu shaka tsafi na aiki, ba shi da masaniya kan abin da ya ke cewa," a cewar wani mai shago da ke bayyana ra'ayinsa a fusace.
A aljihunsa akwai bakar laya, da wata 'yar leda da ya kula abubuwan tsafi, da ya ce na ba shi kariya. Sai dai ya ce ba shi da ra'ayin fitowa filli don nuna karfinsa ko da biyasan dala dubu shida za a yi.
Yarda da batun sihiri abu ne da Kiristoci da Musulmi duk sun yarda da hakan. Malaman waɗannan addinai na yawaita jan hankali kan addu'a domin cin karfin sihiri.
Akwai fastoci da suka yi arziki ko suka yi fice saboda ikirarin suna da karfi ko iya yiwa mutum sihirin da zai kawar da tsafi ko yaƙar maita ko aljannu, abin da wasu malaman addinin Islama ma ke yi.
Sai dai, babu wanda ya karɓi ƙalubalen Mista Adewoyin a wurare biyu da ya ziyarta a Ogun da Ibadan, kuma da alama ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen zuwa wuri na gaba a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Yayin da wasu ke watsi da batunsa ake ganin kawai kokari ne na neman jan hankalin mutane, babu wanda zai kawar da kai ko gujewa batun gawarwarkin da aka tsinta babu sassan jiku a yankuna da dama.

Kashe mutane domin amfani da sassa jikinsu don tsafi ya jefa Najeriya cikin tashin hankali a shekarun 1990 abin da ya kai ga tarzoma a gabashin birin Owerri bayan garkuwa da kashe wani yaro ɗan shekara 1996.
Yanzu da zuwan kafofin sada zumunta da wuya a wayi gari ba a samu labarin ɓacewar mutum ko hoton mutumin da aka kashe da yanka wani sassa na jikinsu domin tsafi.
A watan da ya gabata an yi wani tashin hankali bayan an zargi wasu mutum uku da kashe wata yarinya 'yar shekara 17 a jihar Ogun domin amfani da sassa jikinta don tsafin arziki.
Sun amsa laifin kisa bayan cafke su da 'yan sanda suka yi da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Cafke su dauke da tukunyar kasa da jan kyale kusan kamar abu ne da aka saba gani a wasan kwaikwayon Nollywood, Fitacciyar masana'antar shirya fina-finai da ke nuna irin wannan tsubuce-tsubuce, sai dai wannan gaskiya ne.
Akwai maza matasa - wanda shekarunsu bai haura 21 ba, sun asassa maudu'in #At21, inda suke bayyani kan abubuwan da suke yi a cikin al'umma domin su yi kudi cikin gaggawa.

Asalin hoton, AFP
Mutuwar yarinyar ta kai ga bude kofar muhawara a majalisar dokoki kan tsafi inda suke ganin akwai bukatar a ayyana dokar ta baci kan kashe mutane domin tsafi", kamar yada suke gani da koya daga fina-finan Nollywood a cewarsu.
Ministan yaɗa labarai Lai Mohammed ya yi tsokaci kan batun, inda suke daura alhaki kan fina-finan Najeriya da kafar sada zumunta kan assasa kashe-kashe.
Yana son hukumar tace fina-finai ta tursasawa masu shirin fim tsame irin wadanan labarai da ke magana kan kudin tsafi.
Sai dai masu shirya fina-finai ba su fahimci hakan ba - suna ganin kawai ana so a yi amfani da masana'antarsu ce wajen daura laifi.
"Ministan ya yi batan hanya, ba zai yiwu ya yi amfani da 'yancin mu wajen ba ta mana sana'a ba," a cewar mai shirya fim kuma mai fitowa a fina-finai Kanayo O Kanayo.
Ya ce ministan na kau da kai daga abubuwan da ke addabar al'umma da iyalai, da sarakunan gargajiya da al'adu da 'yan siyasa, da suke ke tasiri a zukata matasa.
Yayin da ake tafka muhawara kan wanda za a daurawa laifi kashe-kashe, akwai bukatar ji daga bangarori daban-daban na kasar kama daga fanin ilimi.
Akwai dai gazawa wajen fadakar da mutane ainihin gaskiya kan batun tsafi da tsubuce-tsubuce, a cewar Mr Adewoyin.
Yana fatan cewar zagayensa na nuna tawaye ya fallasa abin da ya kira kareraye da yaudara kan tsafi da tsubu, domin kawo karshen kashe-kashe don tsafi da sassan jikin mutane.
"Ya ce rashin tunani ne mutum ya yarda da cewa ɗan adam na iya sauyawa zuwa doya ko ayaba, akwai damuwa cikin irin wadanan tunani da yarda da mutane ke da shi," a cewarsa.












