Yadda masu acaba da masu tasi ke cin zarafin mata a Kenya

Asalin hoton, Getty Images
A cikin jerin wasiƙu daga marubuta 'yan Afirka, mai watsa labarai daga kasar Kenya Waihiga Mwaura, ya duba wani sabon abin fusata da ake zargin wasu masu tuka baburan tasi ke yi, kana ya tambayi dalilan da suka sa yake da matukuar wahala a dauki mataki a kansu.

Ga duk wanda ke tuki a babban birnin kasar Kenya ya san ya kamata su fahimci baburan tasi - da aka fi sani da boda-boda.
Da farko za ka iya fara jin karan injin na sauya amo a lokacin da matukin babur din ke kara wutar tafiya, kana watakila ka hanagi wani abu ta cikin madubi - kamar irin rigar jaket din nan mai kyalli ki kuma hular kwano mai launin rawaya.
Ba tare da bata lokaci ba za ka gan su a kusa da kai - kusa da gefen motarka, suka shiga gabanka suna tsallake hanyarka.
Da zarar sun buga maka mota, kafin ka kalubalance su sun rika sun yi nisa - ko kuma mafi ban haushi akan yi sa-in-sa.
An bayyana cewa wata takaddama bayan wani hadai da kuma cin zarafin wata mace mai tuka mota da ya haifar da yin Allah wadai a kan matuka baburan tasi din da aka fi sani da boda-boda.
Wani faifen bidiyo game da faruwar lamarin da ya karade ko ina, yanuna matar na ta ihun neman dauki bayan da aka yi mata tsirara tare da tattaba jikinta.
An samu cafke mutane, tare da yin tofin Allah tsine da kuma yin kiraye-kirayen daukar matakai a kan masana'antar matuka baburan boda-boda.

Asalin hoton, Reuters
Amma wannan ba shi ne karon farko da irin wannan hari ya taba faruwa ba.
Baya a cikin shekarara 2014 masu zanga-zanga sun hallara a birnin Nairobi don nuna goyon bayansu ga matan da aka ci zarafi da akai wa hari da yi musu tsirara da wasu akaa bayyana wasu gungun maza suka yi, don kawai ta saka gajeren siket.
Zanga-zangar ta samu halartar dubban mata da suka yi maci a bayan wata tuta da ke ayyana: ''Sutura ta zabina''.
Shekaru shida bayan nan, an yanke wa direban wata karamar motar bas ta haya da yaron motarsa hukincin kisa kan cinn zarafin.
Amma irin wannan nuna fushin kan tsaye ne kawai a kan abubuwan da kyamara ta nuna sun farai ne - ko shakka babu akwai abaubuwan da suka faru da dama da babu kyamara, da bas u karade shafukan sada zumunta ba, kana ba a yi magana a kan su ba.
Tabbas, da alamu 'yansanda kan dauki mataki nan da nan ne da zarar faifen bidiyo ya haddasa nuna fushi - kwanaki uku bayan farmakin.
Wannan jinkiri ka iya nuna tunanin cewa wasu matan sun sha kai koke ga hukumomi game da cin zarafin amma babu wasu matakai kwarara da aka dauka ko kuma bincike sosai.
Kana idan ana magana a kan yin wani abu game da matuka baburun tasi, 'yan siyasa sun nuna a bainar jama'a abu iri daya ne.
Shugaba Uhuru Kenyatta ya bayar da umarnin tsaurara matakai a kan duka masu tuka baburan boda-boda a fadin kasar.
Kana ministan harkokin cikin gida Fred Matiang'i ya ayyana cewa '' dole mu kare hanyoyinmu daga irin wadannan munanan laifuka da ake aikatawa''.

Asalin hoton, AFP
Amma shekaru biyu da suka gabata, ya samu wani rahoto daga hukumar da aka kafa don duba masana'antar tare da kasar takobib daukar mata
A cikin watan Agustan shekarar 2020, ya kafa tsaarin wayar da kai game da ayyukan boda-boda da ke nufin tattara bayanai kan duka matukan a fadin kasar, tare da gyra halayyarsu.
Me ya faru bayan hakan?
Kana da alamu yanzu yana bayyana wa wasu hukumomin, wasu karin shawarwarin yin wani abu.
Daya daga cikin wahalwalun su ne cewa, ga mutane da dama, baburan na boda-bodas sun fi saukin sha'ani na gudanar da al'amura a ko ina.
Suna gamsar da kotomominsu har ma da samar da aikin yi ga dubban matasa.
Duk da haka, Cibiyar Bincike kan aikata Manyan Laifuka ta snara a watan da ya gabata cewa, su kan su babban hadari ne a kan hanyoyin da babu jama'a, kana kadan daga cikin matuka baburan na aikata laifukan fashi da makami, da safarar miyagun kwayoyi har ma da kisan kai.
Baya ga ajiye bayanai a fadin kasa, rahotonnta ya kuma bayar da shawarar horarwa tare da yi wa matuka baburan gawaji.
Akwai wani tsari da kasar Rwanda mawakbciya ta ke amfani da shi, inda ko wane direba mai lasisin tuki, za a bas hi wata na'ura mai iya gano irin abubuwan da suke yi.
Amma duk da haka har yanzu muna cikin wannan hali.
Matsalar cin zarafin mata da ta matuka baburan tasi sanannun abu ne.
Tabbas lokacin fitowa ana nuna fushi ya wuce, yanzu lokaci ne ne daukar matakai.
Amma ina fargabar dole sai mun jira. A yanzu kan ina cike da fatan cewa matar da aka ci zarafi mutanen da ke kaunarta da ke bayar da rahoto a kai, kuma za su taimaka mata ta hanyar abinda ya kasance wani lokaci na abin bakin ciki.ki.










