‘Yan bangar Kenya da ke yakar barayin fiya

An avocado picker in Kenya
    • Marubuci, Daga Emmanuel Igunza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, central Kenya
  • An wallafa

Noman fiya a Kenya ya zama abu mai tsoka ta yadda 'yan daba suka fara mayar da hankali a kansa.

Dalili kuwa shi ne bishiya daya ta fiya za ta iya ninka kudin makarantar yaron da ke zuwa makarantar kudi na duka shekara wanda zai iya kai wa dalar Amurka 600.

Lokacin da buƙatar fiya ke kara yawa a Amurka da Turai, Kenya ta zama kasar da ke kan gaba wajen samar da dan itacen a nahiyar Afrika inda ta zarce Afrika Ta Kudu a bara.

An kafa kungiyar 'yan banga da za ta rika lura da wannan dan itace, wanda ake kira "koren zinare".

Da rana ta fadi, wasu matasa su shida ke yin shigar aiki a wata gona dauke da makamai domin su fara aikin ba ta kariya.

An dauke su haya ne domin su rika kare gonar da wannan dan itace mai farin jini.

Aiki ne mai cike da hadari - za a iya raunata mutum ko kuma a kashe shi sanadin wannan aiki.

Avocado trees
Bayanan hoto, Manoma na gaggawar cire amfanin gonarsu domin kauce wa barayin da suke sace su

Daya daga cikinsu ya shaida mani cewa "ko dai su ku kuma mu, don haka dole mu kare kanmu," yana magana ne kan wani ɓarawo da aka kashe a baya-bayan nan.

Mai gonar da girmanta ya kusa eka ko kuma rabin filin kwallon kafa ya ce dole ne ya dauki mataki saboda ɓarnar da ɓarayin ke masa.

"Za ka iya zagaye duka gonar da shinge amma hakan ba zai hana su yin aikinsu ba," yana nuna wani wuri da aka fasa aka shiga gonarsa.

"Za ka iya kwashe damina guda kana kare kayan amfanin gonarka, cikin ƙanƙanin lokaci ɓarayin su wawashe komai."

Wani dan banga da na tarar yana rufe inda aka fara ya ce, "sai sun ƙara fasawa sun saci abin da suke so."

"Da barci muke yi da iyayenmu ba su samu nutsuwa ba," in ji shi.

Suna lura da gonakin ne da rana.

Ana cirar fiya a Kenya tsakanin watan Fabrairu zuwa Oktoba, amma su ɓarayin har wadanda ba su nuna ba suna sacewa.

A kokarin daƙile kasuwar bayan-fage da ɓarayin ke amfani da ita, hukumomi sun hana fitar da fiya daga watan Nuwamba har sai karshen watan Janairu.

Barin 'ya'yan itacen a jikin bishiyarsu daidai yake da gayyatar barayi.

Jirage marasa matuki

A yankin Meru mai nisan kilo mita 100 ta arewa - lamarin ya fi ƙazanta. Mun isa yankin lokacin da turawan da ke sayan ɗan itace suka je.

Wannan na nufin an bar wasu manoman irinsu Kinyua Mburugu, su cire amfanin gonarsu da wuri.

A rana guda, ana iya nome dubban hectocin fiya, wadanda ake siyarwa a sama da dala 17 ko wanne daya.

Kinyua Mburugu

Ana duba su daya bayan daya domin tabbatar da ingancinsu ga wadanda za su ya sa a cikin kasar, saboda idan aka cire shi da wuri ba ya nuna daga baya.

1px transparent line

A wajen Mburugu, an dauki matakin girbe fiyan da wuri ne domin bai wa ɓarayin ƙafa.

Amma a nan gaba yana da niyyar amfani da wata hanyar zamani domin kare amfanin gonarsa.

Zai sanya kyamarar tsaro a ko ina cikin gonarsa da ta kai eka 10.

Daga zaune a cikin ɗakinsa zai rika ganewa idanunsa abin da ke aukuwa a gonarsa tare da taimakon ɗansa da ya karanci yadda ake daukar fim a jami'a.

"Ɗana ya nemi mu rika amfani da jirage marasa matuƙi ko da yaushe domin lura da gonar," in ji Mburugu.

"Basu da tsada ne?" na tambaya.

"A'a aikin da za su yi ai kwalliya za ta biya kuɗin sabulu.

Mutane za su yi gaban kansu

Muna cikin magana, sai aka kira shi a waya. 'Yan banga sun kama wasu mutane da yawa da suka kama hayar gida a tsakiyar garin Meru, shiri ne na satar fiya da suke yi a nan gaba.

Daga baya sai wani da ake kira Julius Kinoti, da yake jagorantar tawagar masu aikin tsaron, ya ce daga baya sun gano buhunhuna cike da fiya da aka sata.

Map
1px transparent line

Sun shaida wa 'yan sanda abin da ke faruwa, amma sun yi gargadin cewa ya kamata 'yan sanda su dauki matakin da ya dace, domin kada mutane su fara yin gaban kansu.

"A wannan daren muka kama wadannan ɓarayi, idan na hura usur domin sanar da mutane, 'yan ƙauye za su fito ne su kashe su baki ɗaya - atire za a yi musu - saboda mutane sun gama fusata."

Yanzu ne kasuwancin fiya a Kenya ke kanshin dan-goma, hakan ya sa mutane da yawa na ta zuba hannun jari ciki.

A bara, wannan dan itace ya samar wa manoma a Kenya kudin da suka kai dala milyan 132, in ji ma'aikatar kasuwanci ta kasar.