Kogin Yala na Kenya: Mamaki da kaico na kogin Kenya da aka gano gawawwaki

    • Marubuci, Daga Ferdinand Omondi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Yala, Kenya
  • An wallafa

"Na ga fuskar dan uwana. Muna kama da juna ta fuska, har ma ta baki. Na ga kafafunsa ma, ba shakka dan uwana ne."

Kalaman da Irene Waheto ke furtawa ke nan cikin dimuwa bayan da ta fito daga cikin dakin ajiye gawawwaki na asibitin Yala, da ke yammacin Kenya.

Akwai wasu gawawwakin akalla 19 wadanda ba a kai ga gane su ba har yanzu. An tsamo su ne shekara biyu da ta wuce daga kogin Yala da ke kusa, dukkaninsu sun rube.

Ms Waheto tana ta kiran 'yan uwa da danginta da ke Nyeri, wanda gari ne da ke nisan kilomita 300 a gabashin kasar.

Ta ce :"Ndirangu ne na tabbata shi ne," Tana fadin haka tana kuka a waya.

To amma yadda aka yi aka samu gawarsa a wani kogi da ke da nisa daga garinsu shi ne abin da bas u sani ba.

Ms Waheto ta gaya min cewa dan uwanta ya bata a watan Nuwamba na shekarar da ta wuce a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Nakuru daga Nairobi, babban birnin kasar. To amma fa nisan kilomita kusan 200 ke nan daga inda aka samu gawarsa.

Tun daga wannan lokaci danginta suke ta nemansa a ofisoshin 'yan sanda da kuma dakunan ajiye gawawwaki na asibitoci da ke kusa da biranen biyu. Neman nasu ko kusa bai kai ga wannan yanki mai nis ana yammacin Kenya ba.

Sun yanke shawarar zuwa nan su duba gawar dan uwan nasu ne, bayan da a a ranar Litinin wasu masu kare hakkin Dan-Adam suka ce gawawwakin da aka gano a kogin Yala a 'yan watannin nan har yanzu suna dakin adana gawawwaki.

An gaya wa Ms Waheto, wadda tun lokacin da ta yi aure shekara goma baya take zaune a kusa da wurin da ta je dakin ajiye gawawwaki na asibitin Yala ta duba. To amma sai a tunaninta take ganin ya za a yi a same shi a nan wurin da ke da nisa sosai dag inda aka yi masa gani na karshe. To amma abin mamakin a nan aka samu gawar tasa.

Gane gawar ke da wuya sai Ms Waheto ta fadi kasa tana ta kwarmata ihu tana kuka da kururuwa, abin da ya tayar da hankalin dukkan wani da ke kusa da ita.

Ba ita kadai ba ce take neman dan uwanta da ya bace kuma ba ita kadai ba ce take mamakin yadda gawarsa ta kasance a Yala ba.

Ben Chepkwony ya yi tafiyar sama da kilomita 100 yana neman dan uwansa, Philemon, wanda ya bata a watan da ya wuce a lokacin da yake kan hanyarsa tsakanin Nairobi da Nakuru.

Shi ma an samu gawarsa cikin wadanda aka tsamo daga kogin Yala, kuma ganin gawar ya jefa

dan uwansa Mr Chepkwony cikin halin dimuwa, yana kururuwa.

"Ban san wanda yake kisan wadanan mutane yana jefa su a nan ba,'' Abin da yake furtawa kenan yana shisshika.

Ya ce: "Wannan ba kasar Dumukuradiyya ta Kenya da muke fatan rayuwa a ciki ba ce. Na gaji da wannan kasar. Kuma ba zan taba yarda ba sam-sam."

Mr Chepkwony bai fayyace abin da ba zai lamunta da shi ba a kasar. Yana nufin mutuwar dan uwan nasa ko kuma zama a kasar da bata da kashe-kashen mutane ba tare da sanin wani dalili ba ke neman zama ruwan dare.

Akwai zargi da dama cewa 'yan sanda na da hannu a kashe-kashen da dama kuma kungiyoyin kare hakkin dan-Adam na karkata hankalinsu wajen 'yan-sandan kan gawawwakin da aka gano a kogin Yala.

Boniface Mwangi, daya daga cikin 'yan kungiyoyin kare hakkin dan-Adam, biyu da suka fara gano gawawwakin ya fada a wata tattaunawa ta tuwita cewa, babu wani dan Kenya da yake da damar da zai kashe wani mutum kuma har ya iya daukar gawar ya yi tafiya da ita ta nisan kilomita 200 ya jefar da gawar a kogi.

'Mace-mace da ɓata'

Daya dan rajin kare hakkin dan-Adam din da suka gano gawarwakin Khalid Hussein, na kungiyar Haki Afrika, ya ce hakki ya rataya a wuyan 'yan-sanda, ko dai su yi bayani su wanke kansu kan zargi ko kuma su gano wanda ke da alhakin kashe-kashen.

A Kenya jami'an tsaro na daga wadanda ake zargi na farko a kan irin wadannan kasha-kashe da batan mutane, kuma da dalilai masu ƙwari.

Kungiyoyin kare hakkin dan-Adam suna da bayanai da suka tattara na da yawa daga cikin irin wadannan kashe-kashe, wadanda aka danganta da 'yan-sanda.

A 2019, kungiyar Human Rights Watch ta bayar da rahoton cewa 'yan san-sanda sun kashe sama da mutane 21 da suka hada da yara a unguwannin talakawa na Nairobi, kusan ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba illa dai kawai sun zarge su ne da kasancewa masu aikata miyagun laifuka.

Wata hadakar kungiyoyin kare hakkin dan-Adam mai suna Missing Voices, ta tattara bayanai na kashe-kashe wadanda ba kotu ta yanke hukunci ba, inda ta ce 'yan Kenya 167 ko dai aka kashe ko kuma suka bata tsare a wurin 'yan-sanda a 2020

Yanayin da aka samu gawawwakin da aka tsamo daga kogin shi ma ya sa kokwanto.

Daya daga cikin masu ninkayar da suka gano gawawwakin tare da tsamo su daga kogin ya ce wasu an cusa su aka dinke su a cikin buhu.

Wasu an sanya musu leda a ka, wanda duk wannan na nuna alamu ne cewa an gana musu azaba ne suka mutu, in ji kungiyar Haki Afrika.

"Nauyi ya rataya a wuyn gwmnati ta yi wa al'umma bayan ikan abin da ke faruwa,'' in ji mai rajin kare hakkin dan-Adam Fred Ojiro.

"Gawawwakin da aka gano daga kogin Yala bad aga nan suke ba. Daga nesa suke. Ba mace-mace ba ne na Allah da Annabi. Dole ne gwamnati ta fito fili ta yi bayani kan yadda ake samun wadannan tarin gawawwaki a nan."

Duk da zargin da ake yi babu wata sheda da ke danganta jami'na tsaro da wata daga cikin gawawwakin nan da aka gano a kogin Yala.

'Yan-sanda sun ce wasunsu zai iya kasancewa ruw ne ya ci su ko kuma wasu miyagu ne suka kasha su, amma dai sun fara gudanar da bincike a kai.

Al'umma na kara harzuka tare da neman hukumomi su yi bayani kan kashe-kashe da ɓatan mutane.

Ana sa ran kwararru masu bincike kan gawa su taimaka wajen gano gawawwakin abin da babban jami'in 'yan-sanda Michael Muchiri,y ace yadda wasu gawawwakin suka rube da yadda wasu gawawwakin suka biyo ruwa daga nesa ka iya sa da wahala a iya aikin.

Ya ce : "Yawanci muna dogara ne ga hoton zanen yatsu, wanda muke aikawa ga cibiyar mu ta tattara bayanai da ke Nairobi, to amma idan ba zanen yatsun aikin zai yi wahala sosai.''

Wani jami'in 'yan-sandan Charles Chacha, ya gaya wa BBC cewa abin yan aba shi takaici da bata masa rai yadda duk mutumin da ya bata sai a danganta lamarin da jami'an tsaro.

'Yan-sanda sun ce gawawwakin da ba a zo an karba ba sun taru ne tsawon shekara biyu, ba wai kawai a 'yan watannin nan aka gansu ba, amma kuma na ga wasu Karin gawawwakin biyu a kogin.

Irin doyin da ake ji a kusa da bakin kogin ne ya sa aka gansu.

Daya ma ta zagwanye har ta kusa zama kwarangwal. Dayar kuma da ke kusan nisan mita 300 a tsakani, ta wani namiji ce, ta makale a tsakanin duwatsu, da suka hana ta gangarawa.

Yanzu dai wasu iyalan a Kenya za su iya samun bayanai kan inda 'yan uwansu da suka bata suke, to amma wadannan bayanai za su kasance dan wani bangare ne kawai na tarin bayanai masu sarkakiya na mutane da yawa da suka bace.