Matan da ke fuskantar barazanar fyaɗe a Clubhouse

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Karishma Patel
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
A watan Nuwamba, abokan Bhavini sun aika mata da wasu batutuwa da aka tattauna waɗanda aka naɗa daga manhajar Clubhouse inda aka tattauna kan irin kayan da ta saka.
Manhajar Clubhouse tana bayar da dama ga masu amfani da ita su yi zumunci ta hanyar saƙon murya kai tsaye a tattare.
A cikin saƙon da aka aika mata, maza suna ta gwanjon sassan jikin matan har da nata.
Sai dai Bhavini wadda ke zaune a India kuma wadda sunanta aka ɓoye shi domin kare ta, ta ce ba ta yi mamaki ba.
"Maza sun shafe watanni suna ci mani mutunci a manhajar, inda suke buɗe ɗakunan tattaunawa da sunana aƙalla sau ɗaya a mako inda suke kirana da sunaye marasa daɗi.
Wannan ne sakamakon da za ki samu idan kin kasance mai yawan magana," in ji matar mai shekara 33 wadda ke bincike kan tsare-tsare.
Tana daga cikin aƙalla mutu huɗu na ƙabilar Hindu wadda aka yi gwanjonta a irin wannan rahar da ake yi a Clubhouse na tsawon sa'o'i biyu inda sama da mutum 200 suka rinƙa sauraren tattaunawar da ake yi a lokacin.
Clubhouse ya shaida wa BBC cewa a ranar da lamarin ya faru, ya dakatar da shafukan waɗanda suka aikata wannan lamari da kuma buɗe ɗakin da aka yi gwanjon a manhajar tare da yi musu gargaɗi.
Matar ta bayyana cewa ƴan ƙabilar Hindu da dama ana neman su da irin wannan sharri, inda ake kiransu da masu cin amanar ƙasa domin sun ta caccakar firaministan India Narendra Modi da kuma jam'iyyarsa ta BJP.
Ba su kaɗai bane ke fuskanatar irin wannan cin mutunci ba. Mata Musulmai da ke zama a India, waɗanda da dama daga cikinsu suke yawan sukar gwamnatin su ma duk an rinƙa baje kolinsu a shafukan sada zumunta sama da wata shida, wanda hakan ya ja aka kama mutane da dama.
Sai dai a duk irin wannan gwanjon da waɗannan mutanen suka rinƙa yi, babu wanda za a ce an sayar da gaske - babban burin yin hakan shi ne a ci mutuncinsu a hana su magana.
Masu sharhi sun ce matan da ake cin mutunci, musamman Musulmai adadinsu ya ƙaru a ƴan shekarun nan a ƙarƙashin mulkin Jam'iyyar BJP. Suna zargin jam'iyyar da amfani da soji domin yaƙar duk wanda yake adawa da tsare-tsaren Mista Modi.
Sai dai Jam'iyyar BJP ta musanta waɗannan zarge-zarge, shugabannin jam'iyyar ba su cika Allah-wadai da cin mutuncin matan da ake yi ba, duk da idan aka duba shafukan waɗanda suke abin za a ga magoya bayan jam'iyyar ne ko kuma ma'aikatanta.
Shi kansa Mista Modi ɗin an tambaye shi me yasa yake bin wannan lamari a shafin Twitter.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da an samu irin wannan matsala kuma ana kan samu a shafin Twitter, ana ci gaba da irin wannan cin mutunci a wasu manhajojin waɗanda jama'a ba su cika amfani da su ba kuma wanda yake da wahala a gano masu su.
A lokacin da Bhavini da wata mata Rekha suka shiga manhajar Clubhouse a 2021, sun shiga da niyyar yin magana ne cikin kwanciyar hankali a kan manhajar kan siyasa.
Manhajar ta Clubhouse ta yi suna ne ba wai a matsayin wajen zumunci da tattaunawa ba kai tsaye, amma ana amfani da ita wajen jin maganganun manyan mutane na duniya irin su Drake da Oprah da Elon Musk.
Sai dai matan biyu sun gano cewa tattaunawa kan batun siyasar India abu ne mai wahala - ko dai kan batun goyon bayan da suke ba manoma, waɗanda sama da shekara guda suke ta yajin aiki kan sabbin dokokin noma da Mista Modi ya saka.
"An soma cin zarafin a ranar da na soma tofa albarkacin bakina," in ji Rekha, wata shahararriya a fannin komfuta wadda ita ma shekarar ta 33.
Ita da Bhavini sun bayyana cewa masu cin mutuncinsu sun buɗe shafuka da hotunansu tare da yin barazanar fyaɗe.
"Har a wani lokaci, duk lokacin da na shiga ɗakin tattaunawa wani kan yi magana da bakinsa ya zage ni ya ce na fita," in ji Bhavini. "Akwai shafuka huɗu na bogi da aka buɗe da sunana."

Asalin hoton, Getty Images
Bhavini da Rekha sun bayyana cewa sun kai ƙarar ɗakunan da kuma masu shafukan sau da dama amma duk da haka masu cin mutuncin na nan.
"Hakan na kama da bai wa mutane dama su yi barazana ga mutane," in ji Rekha.
Wata sanarwa da Clubhouse ɗin ya fitar ya bayyana cewa manhajar "ta gudanar da bincike mai zaman kansa da kuma gano cewa duka mutum biyun sun kai ƙara a baya ga Clubhouse da wasu ɗakunan, waɗanda suka karɓa da martani a rubuce".
Bhavini ta bayyana cewa mazan da suka shiga wannan tattaunawar sun yi magana a kan ƙirjinta inda suka yi amfani da wasu hotuna. An ɗauko waɗannan hotunan ne daga shafinta na Instagram a wasu hotuna da ta saka wata rigar ninƙaya.
Rekha ta shiga ɗakin tattaunawar na wasu mintoci sai ta ji maza na ta ƙyarƙyata dariya kan batun ƙirjinta.
Ta ji mutane na ta batun tarawa da ita tare da yin kalaman batsa kanta da wasu mata da kuma yin muggan kalamai kan ƴan Pakistan da addinin Sikh.
"Na ji an tozarta ni. Wannan ne abu mafi muni da na taɓa ji a kaina, ana tallata al'aura ta."
Rekha, wadda a baya ta rinƙa rarraashin wata ƙawarta Musulma wadda ba da daɗewa ita ma aka yi gwanjonta, sai ga shi ita ma hakan na faruwa da ita.
"Ana tafiyar da mata kamar kayayyaki a India, ko a ɗaukaka su ko a sayar da su a lokacin da ake so."
Bhavini da Rekha nan take suka kai ƙara wannan ɗakin tattaunawar, amma an ci gaba da tafiyar da ɗakin na aƙalla sa'o'i biyu.

Asalin hoton, Getty Images
BBC ta kuma gano akwai aƙalla mutum ɗaya wanda ke amfani da manhajar Clubhouse wanda ke da alaƙa da gwanjon matan wanda yana ci gaba da cin karensa ba babbaka a manhajar inda yake amfani da wani shafin na daban wanda aka buɗe a ranar da aka yi gwanjon.
"Ko sau nawa na kai ƙarar shafi, babu abin da ke sayawa," in ji Rekha.
Ana ta nuna damuwa kan yadda za a tabbatar an kama mutum da laifi a a shafin tunda mutane ba za su iya duba abubuwan da suka tattauna a baya ba - ba a naɗar su ana ajiye su domin amfani a gaba.










