Omicron: Me ya sa mutanen da suka yi rigakafi suke sake kamuwa da korona?

An wallafa

Duniya na fuskantar yaɗuwar wani sabon nau'in annobar cutar Covid-19.

Ƙasashe irin su Amurka da Faransa da Birtaniya da Ajantina da Brazil da sauran su na samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar saboda yaɗuwar nau'ukan delta da omicron.

Sai dai masana kimiyya da likitoci da cibiyoyin lafiya na ci gaba da dogaro kan rigakafi daban-daban da ake da su wadanda an riga an gwada kuma duniya ta yarda da su don samun kariya daga cutar.

A wannan maƙalar mun yi duba kan yadda rigakafin ke taimakawa wajen daƙile annobar.

Labaran ƙarya na samun gindin zama

Ganin yadda ake samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar a ƙasashe irin su Amurka da Faransa da Birtaniya, sai labarin sahihancin rigakafin ya sake zama wani babban maudu'in da aka fi tattaunawa a kansa a shafukan sada zumunta.

A yayin da wasu masu amfani da shafukan suke sukar matakan da hukumomi ke ɗauka don goyon bayan rigakafin, wasu kuma sun mayar da hankali ne kan tattauna illolin da rigakafin ke da shi.

Zuwa yanzu dai ba a gano wasu manyan illoli tattare da rigakafin ba, in aka ɗauke ƴan ƙanana da su ma suke ɓacewa cikinƴan kwanaki kaɗan.

Daga cikin wasu ƙorafe-ƙorafen da ake samu sun hada da yadda wajen da aka yi allurar ke yi yin ja kuma ya yi ta ciwo, da masassara da ciwon kai da gajiya da ciqwon jiki da jin sanyi da kuma tashin zuciya.

Wasu illolin da suka fi zafi sun haɗa da daskarewar jini da kumburin wani sashe na zuciya, kuma hukumomin lafiya sun ce ba a cika samun irin su ba, sannan amfanin yin rigakafin ya fi illolinta yawa a cewarsu.

BBC ta zanta da Renato Kfouri, wani likitan yara da cututtuka masu yaɗuwa a kan tasirin rigakafin da ƙarfinsu da kuma yadda aka yi waɗanda suka yi rigakafin suke kuma kamuwa da cutar ta korona.

Ya ce rigakafin cutar korona da aka fara yi na farko-farko da suka haɗa da na kamfanonin Pfizer da AstraZeneca da kuma Janssen da sauran su, an yi su ne don rage barazanar ɓullar nau'ukan cutar mafiya illa, waɗanda ake alaƙanta su da kwantar da mutrum a asibiti da kuma mace-mace.

"Rigakafi sun fi ba da kariya sosai ga nau'ukan cutar da suka fi muni fiye da wacce take kama mutane sama-sama." a cewar Kfouri, wanda darakta ne a Kungiyar Rigakafi ta Brazil.

Maƙasudin waɗannan rigakafi shi ne ba don ya hana yaɗuwar cutar ba ne kwata-kwata, sai don su hana cutar yin mummunan tasiri a jikin mutum.

Irin wannan dalilin ne ya sa aka samar da rigakafin mura, waɗanda ake da su gwamman shekaru da suka wuce.

Rigakafin murar da ake yi duk shekara, ba wai don ya kare mutum daga kamuwa da murar ba ne kawai, sai don ya hana murar yin mummunar illa da tasiri ga wasu rukunin mutane da murar ke saurin kassarawa, kamar yara da mata masu ciki da kuma tsofaffi.

Idan aka duba lamarina bude sosai, wannan kariya daga nau'in cutar mafi illa yana da tasiri kai tsaye ga kafatanin tsarin kiwon lafiya; rage ƙarin cutar a kan hanyoyin numfashi na tafiya kafaɗa da kafaɗa da raguwar cunkoso a ɗakunan gaggawa na asibitoci, da samun isassun gadajen majinyata da kuma samun isasshen lokaci ga tawagar ma'aikatan lafiya da za su duba majinyata yadda ya dace.

Kuma dukkan bayanai sun nuna cewa rigakafi na taka muhimmiyar rawa a wannan fanni sosai; acewar Asusun Ƙuniyar Ƙasashen Renon Ingila Commonwealth, rigakafin cutar korona daga watan Nuwamban 2021 ya kare mace-mace miliyan 1.1 da kuma rage yawan waɗanda cutar ta kwantar a asibiti a kalla miliyan 10.3 a Amurka kawai.

Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta Turai (ECDC) da Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO sun yi ƙiyasin cewa an ceto rayuwar mutum 470,000 da suka haura shekara 60 a ƙasashe 33 a faɗin nahiyat Turai tun bayan da aka fara yi wa mutane rigakafin.

Wane abu ne ke bayyana yanayin da ake ciki a yanzu?

Babu ƙarya cewa mutanen da aka yi wa rigakafin na sake kamusa da cutar a baya-bayan nan, kuma za a iya bayyana hakan ta fuska uku.

Na farkon mai sauƙi ne: mutane a faɗin duniya sun taru a wurare a cunkushe don yin bukukuwan Kirsimeti da na Sabuwar Shekara. Wannan abu shi kaɗai ya ƙara barazanar yaɗuwar cutar korona.

Abu na biyu, kusan shekara ɗaya bayan da rigakafin ya wadata a wasu sassan duniya, ƙwararru sun gano cewa kariyar da ake samu daga cutar korona bayan yin rigakafi ba ya tasiri na har abada.

"Kariyar da ake samu na raguwa cikin wucewar lokaci. Wannan raguwar na iya kasancewa mai yawa ko kaɗan ya dangata ne da irin rigakafin da mutum ya yi da kuma yanayin kowane mutum," kamar yadda Kfouri ya bayyana.

"Wannan ce ta sa ake da buƙatar yin rigakafin karo na uku, a fara da tsofaffi sai waɗanda suke da ƙarancin garkuwar jiki sai kuma sauran al'umma baki ɗaya" a cewar likitan.

Abu na ukun kuma yana da nasaba da ɓullar nau'in omicron na cutar, wadda ta fi saurin yaɗuwa wacce kuma ko da garkuwar jikin da ta karɓi rigakafin bai cika yin tasiri a kanta ba.

"Da wannan muke cewa a yanzu ba zai dinga zama abin mamaki ba don mutanen da aka yi wa rigakafi sun sake kamuwa da cutar korona, kuma dole mu koyi yadda za mu dinga zama da wannan yanayin." in ji Kfouri.

"Sai dai cikin sa'a, ƙaruwar masu kamuwa da cutar da ake yi a baya-bayan nan bai yi muni ba tun da bai zo da ƙaruwar mace-mace da kuma kwanciyar asibiti ba, musamman ga mutanen da aka riga aka yi wa rigakafin," ya ce.

"Rigakain na ci gaba da kare sauran nau'ukan da ke da hadari, kamar yadda ake zato, ya kara da cewa.

Wani bayanin da hukumar laiya ta birnin New York ya nuna yadda ake samun tasirin rigakain ga wadanda aka yi wa, ya kuma nuna banbancin kamuwa da korona, yadda ake kwantar da mutane da kuma yadda suke mutuwa tsakanin wadanda aka yi wa da wadanda ba su yi ba.

A arkon watan Disamba, An samu karuwar wadanda ake kwantarwa da masu mutuwa tsakanin wadanda ba a yi wa rigakain ba, amma a bangaren wadanda suka yi babu wani irgicin masu kamuwa. Za a iya ganin haka karara a wadannan hotunan uku na gaba.

Hoton farko ya nuna yadda adadin masu kamuwa ya karu daf da kashen watan Disamba, da kuma wagegen gibin da aka samu tsakanin wadanda aka yi wa da wadanda ba a yi wa ba.,

A zane na biyu, za mu ga yadda aka rika samun karuwar wadanda ake kwantarwa cikin gaggawa tsakanin wadanda ba a yi wa rigakafin ba, amma hakan bai nuna ainihin yadda abin yake ba.

Kwantar da mutane ya karu sama da yadda ake tsammani.

Hoto na uku ya nuna yadda aka rika samun mutuwar wadanda ba su yi rigakfin ba a New York a watan Disamba, amma an samu karuwar tsakanin wadanda aka yi wa a karshen maki na biyar na watan Disamba, kan daga bisani ya fara raguwa.

Daga karshe dai za mu ahimci cewa wadanda aka yi wa rigakafin korona ba su fiye kamuwa ba da cutar, ba a kwantar da su kuma ba sa mutuwa kamar wadanda ba a yi wa ba.

A kuma adin kasar baki daya, bayanan da aka samu daga hukumar yaki da cutuka masu yaduwa suma sun nuna irin wannan sakamako.

A rahotannin baya-bayan nan hukumomin laiya a Burtaniya sun nuna an samu irin wannan sakamako.

Bincike na biyu, da hukumar ta yi da kanta ya nuna, duka rigakafi ukun da ake da su suna aiki da yakai kashi 88 cikin dari, sai dai har yanzu ba ta yi bayani kan har zuwa yaushe aikinsu zai kare ba, amma tace inda bukatar sake yin wadda za ta kara ba da garkuwar jiki za a yi a Watanni masu zuwa.

Ga Kouri kuwa, duka wadannan shawarwarin ana kara jaddada mahimmancinsu ne kawai saboda nau'in Omicron da kuma karuwar wadanda suke kamuwa da ita.

"Kuskure ne a ce babu wani amanin yin rigakafin saboda in ba haka ba kowa zai kamu da cutar. Rigakfin na na mayar da cutar ta koma wani karamin abun da zai wadda za a iya magancewa gada gida cikin sauki a ko wanne lokacin," in ji shi.

"Za mu iya fita daga kangin wannan annobar ne kawai da yawan rihgakafin da ake yi wa jama'a ciki har da kananan yara, da girmama dukkan dokoki kamar sanya takunkumin da ba da tazara da rashin gudanr da taruka da wanke hannu," in ji masanin.